Haiti : An Zabi Jocelerme Privert A Matsayin Shugaban Wucin Gadi
https://parstoday.ir/ha/news/world-i751-haiti_an_zabi_jocelerme_privert_a_matsayin_shugaban_wucin_gadi
Mr Privert ya maye gurbin Michel Martelly da ya kawo karshen wa'adin mulkin sa a ranr 7 ga watan Fabariru, ba tareda mika ragabar mulkin ba ga wani.
(last modified 2018-08-22T06:57:48+00:00 )
Feb 14, 2016 09:02 UTC
  • Haiti : An Zabi Jocelerme Privert A Matsayin Shugaban Wucin Gadi

Mr Privert ya maye gurbin Michel Martelly da ya kawo karshen wa'adin mulkin sa a ranr 7 ga watan Fabariru, ba tareda mika ragabar mulkin ba ga wani.

A kasar Haiti yan Majalisun kasar sun zabi Jocelerme Privert a matsayin Shugaban wucin gadi.

Jocelerme Privert, dan shekaru 62 a duniya an zabe shi ne a zagaye na biyu na zaben da 'yan majalissun kasar suka gudanar a cikin daren jiyya Asabar.

Wannan dai shi ne karo farko da aka zabi wani shugaban kasa ta hanyar majalisa a tarihin kasar.

Mr Privert ya maye gurbin Michel Martelly da ya kawo karshen wa'adin mulkin sa a ranr 7 ga watan Fabariru, ba tareda mika ragabar mulkin ba ga wani.