Barka da sallah na Shugaban Rasha ga musulmin kasar Sa
Shugaban Kasar Rasha ya yiwa Al'ummar musulmin kasar sa barka da sallah.
A cikin wani bayyani da ya fitar yau talata, Shugaba Viladimin Putun ya ce Al'ummar musulmin kasar na taka muhimiyar rawa wajen samar da soyayar juna a tsakanin kabilun kasar
Musulimin Rasha sun yi riko da kyauwawen al'adu na Addini wanda tahiri ya nuna cewa a irin wannan lokaci na bukukuwan karamar sallah suna shirya bukukuwa masu ma'ana tare kuma da taimakawa masu karamin karfi, sannan kuma suna kaiwa 'yan uwa da aminan arziki musulmi da wadanda ma ba musulmi ba ziyara a irin wannan lokaci.
Shugaba Putun ya ce Al'ummar musulimin kasar suna bayar da muhimiyar gudumuwa wajen gina kasar, daga ciki har da gine-gine jami'o'i da cibiyoyin ilimi, kuma wannan gudumuwa da ya kamata ko wata Al'umma ta bayar wajen gida da kuma ci gaban kasar ta.
A yau ne dai Al'ummar musulmin kasar Rashan suka gudanar da sallar idi a cikin manyan masallatai da cibiyoyin addini da adadinsu ya haura dubu bakwai.