Hukuncin Dauri Na Watanni 21 kan Messi
https://parstoday.ir/ha/news/world-i7735-hukuncin_dauri_na_watanni_21_kan_messi
Wata Kotu a kasar Spain ta yanke hukuncin dauri na tsawon watanni 21 akan shahararren dan wasan Barcelona Lionel Messi da mahaifinsa, saboda samun su da laifin yin coge wajen biyan haraji.
(last modified 2018-08-22T11:28:33+00:00 )
Jul 06, 2016 18:05 UTC
  • Hukuncin Dauri Na Watanni 21 kan Messi

Wata Kotu a kasar Spain ta yanke hukuncin dauri na tsawon watanni 21 akan shahararren dan wasan Barcelona Lionel Messi da mahaifinsa, saboda samun su da laifin yin coge wajen biyan haraji.

Hakazalika kotun ta bukaci mutanen biyu su biya tarar wasu kudade Euro milyan 3 da dubu 700 saboda wannan laifi da suka aikata tsakanin 2007 da 2009.

To sai dai an bai wa mutanen biyu damar daukaka kara a gaban kotun kolin kasar Spain.

Wannan dai ba shi ne karo farko ba da ake daure shahararun 'yan wasa ba saboda kaucewa biyan haraji, inda a wannan shekara irin wannnan hukuncin ya shafi 'yan wasa irin su Boris Becker dan wasan tennis din nan na kasar jamus da Diego Maradona.