Majalisar Kungiyar Tarayyar Turai Ta Yi Allawadai Da Masarautar Bahrain
https://parstoday.ir/ha/news/world-i7765-majalisar_kungiyar_tarayyar_turai_ta_yi_allawadai_da_masarautar_bahrain
Kashi 81% na dukkanin mambobin majalisar kungiyar tarayyar turai sun kada kuri'ar amincewa da wani daftarin kudiri, wanda ya yi Allawadai da kakkausar murya kan cin zarafin 'yan adam da kama karya da masarautar Bahrain ke yi kan al'ummar kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:33+00:00 )
Jul 07, 2016 13:07 UTC
  • Majalisar Kungiyar Tarayyar Turai Ta Yi Allawadai Da Masarautar Bahrain

Kashi 81% na dukkanin mambobin majalisar kungiyar tarayyar turai sun kada kuri'ar amincewa da wani daftarin kudiri, wanda ya yi Allawadai da kakkausar murya kan cin zarafin 'yan adam da kama karya da masarautar Bahrain ke yi kan al'ummar kasar.

Jaridar Mir'atul Bahrain da ake bugawa a birnin London na kasar Birtaniya ta bayar da rahoto a shafin na yanar gizo cewa, a zaman da mambobin majalisar kungiyar tarayyar turai a birnin Brussels tare da halartar mambobi 659 a cikin mambobi 751 na majalisar, mambobi 606 sun amince da daftarin kudurin, yayin da 47 suka ka ki amincewa, 6 kuma ba su bayyana ra'ayinsu ba, wanda hakan ke nuni da cewa kashi 81% na dukkanin 'yan majalisar su 751 ko kuma kashi 92% na 'yan majalisar da suka halarci zaman su 659 sun amince da wannan daftarin kudiri.

 

An dai gabatar da wannan daftarin kudirin ne bayan hardahada rahotanni da manyan kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya suka yi da suka hada da Amnesty International da kuma Human Rights Watch da sauransu suka yi kan cin zarafin dan adam da keta huruminsa da gwamnatin Bahrain ke yi saboda dalilai na siyasa da bangaranci na mazhaba, musamman ma mabiya mazhabar shi'a wadanda su ne fiye da kashi 85% na al'ummar kasar ta Bahrain, inda suka yi ishara da matakan baya-bayan na da masarautar kasar ta dauka, na daure babban sakaren jam'iyyar siyasa mafi girama a kasar ta Al-wifaq Sheikh Ali Salman, duk kuwa da cewa dama tsarin kasar bai yarda da mulkin dimukradiyya ba, sai kuma batun kama shugaban cibiyar kare hakkin bil adama a kasar Nabi Rajab, gami da janye izin zama dan kasa daga babban malamin addini na kasar Sheikh Isa Kasim.

 

Wannan mataki na majalisar kungiyar tarayyar da ke yin Allawadai da masarautar Bahrain da ya zo ne a matsayin ba zata ga masarautar Bahrain, inda take ganin hakan a matsayin wani mataki ne juya mata baya daga kasashen turai da take dasawa da su, kuma suke mara mata baya.