Rasha ta kori Jami'an Diplomasiyar Amurka biyu
https://parstoday.ir/ha/news/world-i7852-rasha_ta_kori_jami'an_diplomasiyar_amurka_biyu
Kwana guda bayan da Amurka ta kori Jami'an Diplomasiyar Kasar Rasha guda biyu daga cikin kasar, A wannan Assabar din ita Rashan ta korin Jami'an Diplomasiyar Amurka biyu daga cikin kasar
(last modified 2018-08-22T06:58:34+00:00 )
Jul 09, 2016 11:19 UTC
  • Rasha ta kori Jami'an Diplomasiyar Amurka biyu

Kwana guda bayan da Amurka ta kori Jami'an Diplomasiyar Kasar Rasha guda biyu daga cikin kasar, A wannan Assabar din ita Rashan ta korin Jami'an Diplomasiyar Amurka biyu daga cikin kasar

A cikin Taron Manema Labarai da ya kira a wannan Assabar, Mataimakin Ministan harakokin wajen kasar Rasha Sergueï Riabkov ya ce an samu Jami'an Diplomasiyar na Amurka ne da lafin karya dokokin kasar da kasa

Rahoton ya ce Jami'an Diplomasiyar na Amurkan da aka kora manbobin kungiyar Leken asirin Amurka ne da ake kira da CIA kuma daya daga cikin su har ma ya yi rikici da Jami'in Dan sandar kasar.

Mista Riabkov ya ce suna fatan magabatan Washinton su gyara kura-kuran siyasar su a kan kasar sa, matukar kuma suka ci gaba da irin wadannan kurakuren, shakka babu Masco za ta mayar da martanin da ya dace.

A jiya Juma'a Kakakin Ma'aikatar harakokin wajen Amurka John Kirby ya sanar da cewa Watsinton ta kori Jami'an Diplomasiyar Rashan ne a matsayin mayar da mayar da martani kan harin da Jami'in Dan sanadar Rashar ya kaiwa Jami'in Diplomasiyar Amurka a birnin Mosco ranar 17 ga watan Yunin da ya gabata.

Saidai Kasar Rashan ta ce Jami'in Diplomasiyar na Amurka ya ki nuna katin sa bayan da Jami'in Dan sandar ya tambaye sa, wannan shi ne musababin rikicin na su,har ma Kafafen watsa labaran kasar Rashan sun watsa faifain vidio na rikicin tsakanin Jami'in Diplomasiyar Amurkan da Jami'in Dan sandar na Rasha.