Portugal ta dauki kofin nahiyar Turai
https://parstoday.ir/ha/news/world-i7924-portugal_ta_dauki_kofin_nahiyar_turai
Kasar Portugal ta zamanto zakarar kwallon kafa ta Nahiyar Turai a karo na farko
(last modified 2018-08-22T06:58:34+00:00 )
Jul 11, 2016 01:19 UTC
  • Portugal ta dauki kofin nahiyar Turai

Kasar Portugal ta zamanto zakarar kwallon kafa ta Nahiyar Turai a karo na farko

Portugal ta cinye kofin kwallon kafa na nahiyar Turai, bayan ta doke Faransa da ta karbi bakuncin gasar da ci daya mai ban haushi, wanda Portugal din ta samu nasarar zura kwallon ne a ragar Faransa bayan an kara musu lokacin wasa.

Dan wasan Portugal Eder ne ya jefa kwallon a minti na 110, a wasan da aka yi a dandalin kwallon kafa na Stade de France, kuma da wannan ci daya mai ban haushin aka kamala wasan.

A yayin da magoya bayan Portugal ke murna, magoya bayan Faransa sun nuna takaici da barinsu har ma wasunsu suka fara jifa har saida Jami'an 'yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sanya hawaye wajen tarwatsa su.

Wannan ne dai shi ne karon farko da kasar Portugal ta samu nasarar cin kofin kwallon kafa na Nahiyar Turai.

Masana kwallon kafa da dama sun yi hasashen cewa Kasar Faransa ce za ta lashen kofin,saidai 'yan wasan Portugal sun yi ba-zata sakamakon rawar-ganin da suka taka, duk kuwa da cewa Zakaransu, wato Christiano Ronaldo bai taka-leda zuwa karshen wasan ba saboda raunin da ya ji a wasan rabin lokaci.

'Yan wasan Faransa dai sune suka mamayi wasan, amma ba su samu nasarar jefa kwallo a ragar Portugal ba.