Kasashen Larabawa Da Iran Sun Yi Allawadai Da Harin Nice
(last modified Fri, 15 Jul 2016 11:47:54 GMT )
Jul 15, 2016 11:47 UTC
  • Kasashen Larabawa Da Iran Sun Yi Allawadai Da Harin Nice

kasashen larabawa a sahun gaba Saudiya da kuma Iran sunyi allawadai da harin NIce tare da kira kan a hada kai domin yaki da ta'adanci.

kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran Bahram Qassemi ya ce abun allawai ne wannan harin kuma Iran tana jajatawa al'ummar faransa.

tuni dai shugaban majalisar dokokin faransa Claude Bartolone ya jinkirata ziyara daya shirya kawo wa a makon mai zuwa anan Teheran

wannan dai na zuwa a daidai lokacin da binciken ya nuna cewa wani dan kasar ne ta Faransa dan asalin kasar Tunisiya ya kai harin.

har kawo yanzu dai babu wata kungiya data dau alhakin kai harin.