Karuwar shigar bakin haure a Italiya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i8368-karuwar_shigar_bakin_haure_a_italiya
Hukumar dake sanya ido kan iyakokin kasashen Turai ta sanar da karuwar kwararen bakin haure cikin kasar Italiya
(last modified 2018-08-22T11:28:37+00:00 )
Jul 19, 2016 17:52 UTC
  • Karuwar shigar bakin haure a Italiya

Hukumar dake sanya ido kan iyakokin kasashen Turai ta sanar da karuwar kwararen bakin haure cikin kasar Italiya

A cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Talata, Hukumar ta bayyana cewa idan aka la'akari da bakin hauren da suka shiga kasar Italiya daga arewacin Afirka a watan Yuni da kuma watan Mayu, adadin ya karu da kashi 25% a watan Yuni.
 Hukumar ta kara da cewa a cikin watan Yuni kawai, Bakin haure dubu 22 da 500 ne suka shiga kasar Italiyan ta hanyar  Ruwan Meditrenia kuma aksarinsu 'yan kasashen Najeriya,Sudan da kuma Eritreniya ne.

Hukumar ta kara da cewa 'yan gudun hijrar dake shiga kasar Girka ta hanyar Turkiya sanadiyar yarjejjeniyar da aka cimma tsakanin Buranan Ankara da Bruxul da kuma yadda ake tsananta bincike ya ragu da kashi 95% idan a kwatamta da shekarar da ta gabata.Domin tunkarar kwararen bakin hauren, kungiyar Tarayyar Turai ta cimma yarjejjeniya da Gwamnatin Turkiya, inda ta dauki alkwarin bata  makudan kudade a kan ta hana ficewar bakin hauren zuwa kasar Girka

A bangare guda kuma tsibiran dake kudancin kasar italiya , musaman ma tsibirin Lamfadusa sune yankunan asali da 'yan gudun hijrar kasashen Afirkan ke bi domin shiga kasashen Turai.