An Kori Ma'aikata A Babbar Cibiyar Musulunci Ta Kasar Turkiya
An kori daruruwan ma'aikata a babbar cibiyar musulunci ta kasar Turkiya bisa zargin cewa suna da alaka da juyin mulkin da aka shirya yi a kasar wanda bai yi nasara ba.
Jaridar Hurriyat ta kasar Turkiya ta bayar da rahotoa bugunta na yau cewa, babbar cibiyar musulunci ta kasar Turkiya da ke karkashin kulawar gwamnatin kasar ta sanar da korar ma'aikatanta guda 492 a ciki da wajen kasar, bisa zargin cewa ko dai suna da hannu a cikin yunkurin juyin mulkin, ko kuma sun goyi bayan yin hakan.
Cibiyar da tace duk wanda yake da hannu a cikin wannan lamari yana a matsayin mai cin amanar kasa da al'ummarta, kuma dole a dauki mataki da ya dace a kansa a mahanga ta addini.
Bayanin ya kara da cewa wadanda suka rasa rayukansu daga cikin masu yunkurin juyin mulkin ba za a yi musu sallar janaza ba kamar yadda muslunci ya tanada.