Bom Ya Raunana Mutane 12 A Jamus
A Jamus mutane 12 ne suka raunana bayan da wani matashi ya tayar bom a wani gidan cin abinci dake tsakiyar birnin Ansbach a kudancin kasar.
Matashin wanda aka ce dan asalin kasar Syria ne dake neman mafaka a kasar ya hallaka nan take bayan tashin bom din.
Tuni gwamnatin kasar ta danganta lamarin da harin ta'adanci.
Ministan cikin gida kasar, Joachim Herrmann ya ce matashin dan shekaru 27, wanda akayi watsi da bukatarsa ta zamen mafaka yau da shekara guda na da niyyar hana wani wasa na mawakan ''Pop'' inda mutane sama da 2,000 suka hadu, saidai kasancewar ba shi da tikita bai samu shiga wasan ba.
Saidai ministan ya ce matashin fa, a cen baya ya yi yunkurin hallaka kan sa har sau biyu, kafin daga bisani a dauki yaunin kula da shi a wani asibitin masu tabin hankali.
Wannan dai na zuwa kwanaki kadan bayan da wani matashi mai shekara 18, ya kashe mutum 9 sannan ya kashe kansa a wata cibiyar kasuwanci a binrin Munich.