Majalisar Dinkin Duniya Ta Gargadi Shugaban Kasar Sudan Ta Kudu
Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi shugaban kasar Sudan ta Kudu kan ya guji gudanar da duk wani nade-naden mukamai da suka yi hannu riga da yarjejeniyar sulhun da aka cimma a kasar.
Kakakin Majalisar Dinikin Duniya Farhan Haq a jiya Talata ya yi gargadi ga shugaban kasar Sudan ta Kudu Silva Kirr da ya guji daukan matakin gudanar da nade-naden mukamai a kasar da suka yi hannun riga da yarjejeniyar sulhun da aka cimma tsakanin gwamnatinsa da bangaren 'yan tawayen kasar na dakatar da bude wuta tare da kafa gwamnatin hadin kan kasa.
Farhan Haq ya kara da cewa: Majalisar Dinkin Duniya tana iyaka kokarinta na ganin an mutunta yarjejeniyar dakatar da bude wuta a Sudan ta Kudu tare da ci gaba da gudanar da zaman tattaunawan sulhu da nufin warware duk wata takaddamar siyasa a kasar.
Wannan gargadi na Majalisar Dinkin Duniya ya zo ne a bayan da shugaban kasar Sudan ta Kudu Silva Kirr ya nada Taban Deng Gai a matsayin sabon mataimakinsa bayan da wa'adin sa'o'i 48 da ya gindaya wa mataimakinsa Riek Machar tsohon madugun 'yan tawayen kasar kan ya dawo birnin Juba fadar mulkin kasar ko kuma ya maye gurbinsa da wani mutum na daban, inda wa'adin ya cika a jiya Talata. Riek Machar dai ya fice a birnin Juba ne bayan rikicin baya-bayan nan da ya kunno kai tsakanin sojoji magoyansa da na shugaban kasa da ya kai ga hasarar rayuka.