Turkiyya Ta Yi Allawadai Da Matakin Hana Jawabin Erdogan A Jamus
(last modified Sun, 31 Jul 2016 15:30:55 GMT )
Jul 31, 2016 15:30 UTC
  • Turkiyya Ta Yi Allawadai Da Matakin Hana Jawabin Erdogan A Jamus

Fadar shugaban kasa a Turkiyya ta yi allawadai da matakin da kotun tsarin mulkin Jamus ta dauka na hana watsa wani jawabin shugaban kasar Racep tayib Erdogan kai tsaye ga al'ummar kasarsa dake ganganmi a birnin Cologne na kasar Jamus a yau.

Wannan matakin a cewar kakakin fadar shugaban kasar Ibrahim Kalin abun alla waddarai ne.

Kimanin Turkawa dubu 30 ne da ke goyon bayan Erdogan suka shirya gangami a birnin Cologne na kasar Jamus a wannan Lahadin domin nuna goyan bayan su ga tsarin demukuradiyya a kasar ta Turkiyya bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar 15 ga wata.

A gangamin dai an shirya Erdogan zai yi muhawara ta bidiyo kai tsaye da 'yan kasarsa dake Jamus sai dai mahukuntan kasar suka ki amuncewa bisa fargabar cewa hakan zai iya tada fitina a cikin kasar, lamarin da baiyi wa mahukuntan Ankara dadi ba ko kadan. 

Jamus dai ta kasance kasa data fi yawan 'yan Turkiyya a duniya, inda sama da miliyan daya da rabi ke rayiwa a kasar.