Wani Mutun Ya Raunana 'Yan Sanda Biyu Da Adda A Belgium
'Yan sanda a Belgium sun sanar cewa 'yan sanda biyu ne suka raunana bayan da wani mutun ya sare su da adda a birnin Charleroi dake kudancin kasar.
Mutiman wanda rahotannin suka ce yana ta uhu yana kiran ''Allahu Akbar , Allahu Akbar ya raunana 'yan sanda ne a harabar ofishinsu dake gundumar Charleroi.
Bayanai sun nuna cewa dan sanda guda ya raunana sosai a kusa da fuskarsa, yayin da abokiyar aikinsa ta samu gajeren rauni.
'yan sanda yankin sun ce an raunana mitimin da harbin bindiga da aka masa, kafin daga bisani a sanar da mutuwarsa a wannan gunduma dake nisan kimanin kilomita 60 daga Bruxelles babban birnin kasar.
kawo yanzu dai 'yan sandan yankin sun killace inda lamarin ya auki domin ci gaba da gudanar da bincike.
Koda yake kawo yanzu babu wata kungiya data dau alhakin hakan, sanin kowa ne irin wanan na daga cikin salon da kungiyar 'yan ta'ada ta IS ta bullo dashi domin kai hare haren ta musamen a kasashen Turai.