Cincirindon Magoya Bayan Tsarin Demokradiya A Birnin Istambul
https://parstoday.ir/ha/news/world-i9295-cincirindon_magoya_bayan_tsarin_demokradiya_a_birnin_istambul
Gangamin goyon baya ga shugaban kasar Turkia a birnin Istambul.
(last modified 2019-08-10T14:54:46+00:00 )
Aug 07, 2016 15:18 UTC
  • Cincirindon Magoya Bayan Tsarin Demokradiya A Birnin Istambul

Gangamin goyon baya ga shugaban kasar Turkia a birnin Istambul.

Dubban daruruwan magoya bayan jam'iyya mai mulki a kasar Turkia sun yi gangami a birnin Istambul don nuna goyon bayansu ga tsarin Democradia a kasar da kuma kawo karshen fitowa kan tituna da suke yi tun ranar da aka yi yunkurin juyin mulki a kasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP kafin gangamin na yau a dandalin hadin kai na birnin Istambul, magoya bayan jam'iyyar Justice and Development Party (AKP) suna fitowa kan titunan birnin Islambul da wasu biranen kasar tun ranar 15 ga watan Yulin da ya gabata. 

Gangamin na yau dai a fadin wasu kafafen yada labarai zai kai miliyoyin mutane, sannan an tanaji jami'an tsaro fiye da dubu 15 don tabbatar da tsaron a gangamin. Ya zuwa lokacin bada wannan Labarin dai kamfanin dillancin labaran AFP ya ce tuni mutane dauke da tutocin ja da fari wato tutan kasar ta Turkiya. An kashe mutane 273 a kokarin juyin mulkin da bai kai ga nasara ba, kuma mutane 35 daga cikin wadanda aka kashe masu yunkurin juyin mulkin ne. Har'ila yau an ware wani wuri na musamman ga iyalan wadanda aka kashe a kokarin juyin mulkin a dandalin.