Dawo Da Cinikayya Tsakanin Rasha Da Turkiyya Zai Dauki Lokaci
https://parstoday.ir/ha/news/world-i9391-dawo_da_cinikayya_tsakanin_rasha_da_turkiyya_zai_dauki_lokaci
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya amince da yin aikin da zai dawo da cikakkiyar dangantakar kasarsa da kasar Turkiyya, amma yace dawo da harkokin cinikayya tsakanin kasashen biyu zai dauki lokaci.
(last modified 2018-08-22T06:58:44+00:00 )
Aug 10, 2016 01:00 UTC
  • Dawo Da Cinikayya Tsakanin Rasha Da Turkiyya Zai Dauki Lokaci

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya amince da yin aikin da zai dawo da cikakkiyar dangantakar kasarsa da kasar Turkiyya, amma yace dawo da harkokin cinikayya tsakanin kasashen biyu zai dauki lokaci.

Putin, ya bayyana hakan ne jiya Talata bayan ganawa da takwaransa na Turkiyya  Racep Tayyip Erdogan a birnin Saint Petersburg na Rasha.

A nasa bangare, Erdogan ya fada cewa kasashen biyu zasu dawo da yarjejeniyar cinikayyar da ke tsakaninsu da ta kai $ Biliyan 100. 

Shugaban na Turkiyya ya kara da cewa, a shirye yake ya gina bututun iskar gas da kasar Rasha, kuma zai tattauna da Rasha don ganin Turkiyya ta gina wajen sarrafa makamashin Nukiliya na farko a kasar.

Kasashen biyu dai sun amince da sake wani zama domin samun hanyar da za a kawo karshen yakin da ake A Siriya, duk da cewa suna da sabani ra'ayi akan batun kasar ta Siriya.