Kasar Suizilland ta kori bakin haure kimanin dubu hudu
Dakarun tsaron Suizilland sun ce a cikin wata guda da ya gabata kasar ta mayar da bakin haure dubu hudu zuwa kasar Italiya
A wata sanarwa da ya fitar mai magana da yawun Dakarun kai iyaka na kasar Suizilland David Markuyes ya ce mafi yawan bakin hauren da aka kora sun yi kokarin zama cikin kasar ne bayan da suka shiga da nufin ficewa kuma mafi yawansu sun shigo ne daga kasar Italiya domin haka ne ma Gwamnati ta dauki wannan mataki na mayar da su ta inda suka shigo.
Gidan radion kasar Suizilland ya sanar da cewa daga farkon wannan shekara ta 2016 zuwa yanzu an gano bakin haure sama da dubu 13, domin haka za a fara gudanar da bincike duk dan gudun hijrar da aka tabbatar ya fito ne daga kasashen dake fama da yaki kamar siriya da Iraki to zai iya ci gaba da zama a kasar na wani lokaci.
A nata bangare, Majalisar Dinkin Duniya ta soki matakin da kasar Suizilland ta dauka na korar bakin hauren inda ta ce mafi yawansu masu karamcin shekaru ne kuma an hanasu ganawa da iyayensu.
Majalisar ta tabbatar da cewa kasar Suizilland din wajibi ne ta yi aiki da dokokin kasa da kasa wajen taimakawa bakin haure ba wai ta kore su ba.
A shekarar 1997 ne Kasar Suizilland ta rattaba hanu kan dokar taimakon bakin haure ta Majalisar Dinkin Duniya.