Akalla Mutane 4 Sun Mutu Sakamakon Fashewar Wasu Bama-Bamai
(last modified Fri, 12 Aug 2016 05:01:57 GMT )
Aug 12, 2016 05:01 UTC
  • Akalla Mutane 4 Sun Mutu Sakamakon Fashewar Wasu Bama-Bamai

Rahotanni daga kasar Thailand sun bayyana cewar alal akalla mutane 4 sun rasa rayukansu kana wasu da dama sun sami raunuka sakamakon wasu hare-hare ta hanyar tada bama-bamai a garuruwa Hua Hin, Phuket da sauran wajajen yawon shakatawa na kasar.

Rahotannin sun ce a safiyar yau Juma'a wasu abubuwa sun fashe a a lokuta guda garin na Hua Hin, bayan wasu abubuwan  da suka fashe a garin ajiya Alhamis ma. Har ila yau a  yau din dai wasu an sake jin karar fashewar wasu abubuwan da ake zaton bama-bamai ne a garin Phuket mai wajajen yawon shakatawa.

Rahotannin dai sun ce a sakamakon wadannan fashe fashen bama-bamai mutane hudu sun rasa rayukansu, kana wasu da dama kuma sun sami raunuka.

Rundunar 'yan sandan kasar ta Thailand ta sanar da cewa tuni ta fara gudanar da bincike kan musabbabin wadannan fashe-fashe. Har  ya zuwa yanzu dai babu wani mutum ko wata kungiya da  ta dauki alhakin kai wadannan hare-hare. Sai dai wasu suna zargin 'yan kungiyar aware na kasar masu adawa da sojojin kasar ne suka kai harin.