Rasha : Putin Ya Canza Shugaban ma'aikatansa
https://parstoday.ir/ha/news/world-i9535-rasha_putin_ya_canza_shugaban_ma'aikatansa
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya canza shugaban ma'aikatan fadarsa, Sergie Ivanov, inda ya maye gurbinsa da Anton Vaïno, wanda shi ne mukadashin tsohon shugaban ma'aikatan.
(last modified 2018-08-22T06:58:45+00:00 )
Aug 12, 2016 12:51 UTC
  • Rasha : Putin Ya Canza Shugaban ma'aikatansa

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya canza shugaban ma'aikatan fadarsa, Sergie Ivanov, inda ya maye gurbinsa da Anton Vaïno, wanda shi ne mukadashin tsohon shugaban ma'aikatan.

Sergio Ivanov, dan shekaru 63 na daya daga cikin manyan makusantan shugaban kasar ta Rasha.

Shugaban kasar ta Rasha ya ce Mr Ivanov ne da kansa ya bukaci a sauke shi daga mukamin, saidai tuni masu sharhi kan lamuran yau da kulun a wannan kasa suka danganta hakan da shiryen-shirye akan zaben majalisar dokoki kasar da ke gabatowa da kuma babban zaben kasar na shekara 2018.

Yanzu dai an baiwa Mr Ivanov mastayin mai baiwa shugaban kasar ta Rasha shawar akan harkokin da suka shafi muhalli da sifiri.