An Fara Gudanar Da Yakin Neman Zaben Shugabancin Kasa A Gabon
https://parstoday.ir/ha/news/world-i9586-an_fara_gudanar_da_yakin_neman_zaben_shugabancin_kasa_a_gabon
Hukumar zaben kasar Gabon ta sanar da yau Asabar a matsayin ranar fara gudanar da yakin neman zaben shugabancin kasar a duk fadin kasar a hukumance.
(last modified 2018-08-22T06:58:45+00:00 )
Aug 13, 2016 13:21 UTC
  • An Fara Gudanar Da Yakin Neman Zaben Shugabancin Kasa A Gabon

Hukumar zaben kasar Gabon ta sanar da yau Asabar a matsayin ranar fara gudanar da yakin neman zaben shugabancin kasar a duk fadin kasar a hukumance.

Kamfanin dillancin lbaran Faransa ya watsa rahoton cewa: Hukumar zaben kasar Gabon ta sanar da yau Asabar a matsayin ranar fara gudanar da yakin neman zaben shugabancin kasar har zuwa kwanaki goma sha biyar.

A nata bangaren rundunar tsaron kasar ta Gabon ta yi gargadi kan kiyaye doka da oda a lokacin yakin neman zaben tare da kara karfafa matakan tsaro a kasar.

A gefe guda kuma 'yan adawa suna ci gaba da yin korafi kan yiyuwar tafka magudi a zaben shugabancin kasar kan haka ofisoshin jakadancin Faransa, Amurka da wakilan kungiyar tarayyar Turai da suke Gabon sun fitar da bayanin hadin gwiwa da ke kira ga gwamnatin kasar Gabon kan kiyaye dokokin zabe tare da gudanar da zabuka a kasar cikin yanci da walwala.Ranar 27 ga wannan wata na Ogusta ne za a gudanar da zaben shugabancin kasa a Gabon kuma shugaban kasar mai ci Ali Bango Ondimba yana daga cikin 'yan takara.