MDD: Dubban Mutane Suna Bukatar Taimakon Gaggawa Na Abinci A Nijar
https://parstoday.ir/ha/news/world-i964-mdd_dubban_mutane_suna_bukatar_taimakon_gaggawa_na_abinci_a_nijar
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar dubun dubatan mutane a Jamhuriyar Nijar suna bukatar taimakon abinci na gaggawa da magance irin matsalar rashin abinci da suke fuskanta.
(last modified 2018-08-22T06:57:50+00:00 )
Feb 18, 2016 14:03 UTC
  • MDD: Dubban Mutane Suna Bukatar Taimakon Gaggawa Na Abinci A Nijar

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar dubun dubatan mutane a Jamhuriyar Nijar suna bukatar taimakon abinci na gaggawa da magance irin matsalar rashin abinci da suke fuskanta.

Rahotanni sun jiyo ofishin hukumar kula da kuma tsara lamurran da suka shafi taimakon bil'adama ta MDD (OCHA) da ke birnin Yamai, babban birnin Jamhuriyar ta Nijar, cikin wata sanarwa da ya fitar a yau din nan Alhamis, yana cewa akwai kimanin mutane miliyan biyu da suke bukatar abinci a Jamhuriyar ta Nijar a wannan shekarar ta 2016.

Ofishin ya kara da cewa yana bukatar kimanin dala miliyan 147 don ba da taimakon abinci da wadannan mabukatar da suke a bangarori daban-daban na kasar ta Nijar, sai dai ya ce har ya zuwa yanzu ba a sami wadannan kudaden ba.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Majalisar Dinkin Duniya take sanar da irin wannan matsala da ake fama da ita a Jamhuriyar ta Nijar ba.