Ana Son Haramta Saka Hijabi A Jamus
Ministan cikin gida na Jamus ya nemi da a haramta saka hijabi a kasar, a daidai lokacin da ake ci gaba da tafka muhawara akan hanyoyin inganta tsaro da yaki da tsatsaran ra'ayin addini a kasar.
Bayan tattaunawa da takwarorinsa masu ra'ayin rikau, Mr Thomas de Maizière, ya ce hijibi baya tafiya da tsarin kasarsa wace ke zamen kofa bude ga duniya.
Don haka a cewarsa zasu tattaunawa akan hana saka hijiba a duk wuraren da ake da bukatar hakan kama daga makarantu, jami'o'i wuraren shari'a, idan ana tukida dai saurensu.
ko da yake bai bayanna takamaimai lokacin da matakin zai fara aiki ba, aman ya ce za'a aiwatar da shi mataki zuwa mataki.
Yau ne dai ake sa ran ministan cikin gida na kasar ta Jamus zai yi wani taron manema labarai domin bayyana matakai da kasar ta dauka akan tsaro.