Rasha Na Binciken Wata Sanarwar (IS)
https://parstoday.ir/ha/news/world-i9859-rasha_na_binciken_wata_sanarwar_(is)
'Yan sanda a kasar Rasha sun ce suna bincike kan wata sanarwa da kungiyar IS ta fiyar na cewa iata keda alhakin raunana wasu 'yan sanda kasar biyu a wani hari da adda.
(last modified 2018-08-22T06:58:47+00:00 )
Aug 19, 2016 06:12 UTC
  • Rasha Na Binciken Wata Sanarwar (IS)

'Yan sanda a kasar Rasha sun ce suna bincike kan wata sanarwa da kungiyar IS ta fiyar na cewa iata keda alhakin raunana wasu 'yan sanda kasar biyu a wani hari da adda.

A ranar Laraba data gabata ce wasu matasa biyu suka kaiwa 'yan sanda hari da adda a gundumar Balachikha dake kilomita 20 a arewa maso gabashin Moscow.

'Yan sanda biyu sun raunana sakamakon harin wanda daya daga cikinsu ya ji mumunan rauni.

An dai hallaka maharan biyu, saidai yanzu 'yan sanda kasar sun ce suna ci gaba da bincike kan sanarwar da kungiyar 'yan ta'ada ta IS ta fitar na cewa ita keda alhakin kai harin.