-
Wasu Mahara Sun Kai Hari Kan Wani Sansanin Sojin Afghanistan Da Sanyin Safiyar Litinin
Jan 29, 2018 02:23Rahotanni daga kasar Afghanistan sun bayyana cewar wasu mahara sun kaddamar da wani hari kan wani wajen bincike na sojojin kasar kusa da wani Kwalejin sojin kasar da ke birnin Kabul, babban birnin kasar da sanyin safiyar yau Litinin inda akalla sojoji 2 suka mutu wasu kuma da dama suka sami raunuka.
-
Amurka Na Mutunta 'Yan Afrika Sosai_ Wasikar Trump Ga AU
Jan 28, 2018 11:47Shugaba Donald Trump ya bayyana a cikin wata gajeriyar wasika da ya aikewa shugabannin Afrika cewa '' Amurka tana mutunta 'yan Afrika kwarai da gaske''.
-
Shugaban Kasar Afghanistan Ya Yi Alawadai Kan Harin Da Aka Kai A Birnin Kabul
Jan 27, 2018 15:34Kimanin mutane 95 suka rasa rayukansu yayin da wasu 158 suka jikkata a wani harin bam na kunar bakin wake da aka kai a tsakiyar birnin Kabul na kasar Afghanistan
-
Wasikar Shugaban Amurka Zuwa Shugabanin Afirka
Jan 27, 2018 15:34Cikin wata wasika da ya aikewa Shugabanin Afirka, Shugaban kasar Amirka Donal Trump ya bayyana cewa yana matukar mutumta Al'ummar yankin Afirka
-
Kungiyoyin Ta'addancin Takfiriyya Da Hidimar Da Suke Yi Wa H.K. Isra'ila
Jan 27, 2018 02:24Cikin 'yan kwanakin nan dai kafafen watsa labarai daban-daban suna ci gaba da karin bayani dangane da sabuwar alaka da aiki tare da ke tsakanin haramtacciyar kasar Isra'ila da kungiyoyin ta'addancin 'yan takfiriyya a kasar Siriya bayan da 'Isra'ila' ta kafa wata sabuwar kungiyar ta'addanci a yankin tuddan Golan na kasar Siriya da take mamaye da shi.
-
Shugaban Venezuala Ya Jaddada Aniyar Gwamnatinsa Na Gudanar Da Zabe A Kasar
Jan 27, 2018 02:14Shugaban kasar Venezuala ya jaddada aniyar gwamnatinsa na gudanar da zaben shugabancin kasa a Venezuala duk da matakin da kasar Amurka da kawayenta ke dauka na kunna wutan rikici a kasar.
-
Shugaban Kasar Amurka Ya Sake Maimaita Zarge-Zarge Marassa Tushe Kan Kasar Iran
Jan 27, 2018 02:13Shugaban kasar Amurka ya sake zargin kasar Iran da kokarin mallakar makamin nukiliya tare da jaddada bukatar dakile tasirin Iran a yankin gabas ta tsakiya.
-
Koriya Ta Kudu : Gobara Ta Kashe Mutum 41 A Wani Asibiti
Jan 26, 2018 02:25Rahotanni daga Koriya ta Kudu na cewa mutane a kalla 41 ne suka rasa rayukansu a wata mummunar gobara data kama wani babban asibiti a yankin Miryang dake kudu maso gabashin kasar.
-
Kungiyar AU Ta Bukaci Shugabannin Afirka Da Su Mayar Wa Trump Da Martani
Jan 25, 2018 14:12Shugaban Tarayyar Afirka, Moussa Faki Mahamat, ya kirayi shugabannin nahiyar Afirkan da su mayar da martani ga kalaman batancin da shugaban Amurka Donald Trump yayi wa kasashen Afirkan a kwanakin baya.
-
Kwamitin Tsaron MDD Zai Yi Zama Kan Palastinu
Jan 25, 2018 02:55Mataimakin ministan harakokin wajen Palastinu ya sanar da taron gaggauwa na kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya da zai tattauna kan batun Palastinu.