Kwamitin Tsaron MDD Zai Yi Zama Kan Palastinu
(last modified Thu, 25 Jan 2018 06:25:37 GMT )
Jan 25, 2018 06:25 UTC
  • Kwamitin Tsaron MDD Zai Yi Zama Kan Palastinu

Mataimakin ministan harakokin wajen Palastinu ya sanar da taron gaggauwa na kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya da zai tattauna kan batun Palastinu.

Kamfanin dillancin Labaran Mehr ya nakalto Tisir Jaradat mataimakin ministan harakokin wajen Palastinu na cewa a wannan Alhamis ne, Kwamitin tsaron MDD zai gudanar da taron gaggawa kan Palastinu.

Riyad Mansor wakilin Palastinu a MDD ya bayyana cewa wannan taro na a matsayi tuni ga masu jagorancin  kwamitin tsaron a game kudirin MDD a kan yankin Palastinu.

A ranar 21 ga watan Disamban 2017 da ta gabata ce, Majalisar dinkin duniya ta samar da wani kudiri na goyon bayan Kudus tare da samun amincewar mambobin zauren majalisar 128, da hakan ya tabbatar da cewa Majalisar dinkin duniya ba ta amince da kudirin ayyana birnin Qudus a matsayin hedkwatar haramtacciyar kasar Isra'ila ba.

A ranar 6 ga watan Disamban 2017 ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ayyana birnin Qudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila tare da umarnin Ma'aikatar harakokin wajen sa kasar sa ta fara shirye-shiryen mayar da ofishin jakadancin kasar zuwa birnin Qudus, lamarin da ya fuskanci suka daga kasashen Duniya.