Wasikar Shugaban Amurka Zuwa Shugabanin Afirka
Cikin wata wasika da ya aikewa Shugabanin Afirka, Shugaban kasar Amirka Donal Trump ya bayyana cewa yana matukar mutumta Al'ummar yankin Afirka
Baya ga hakan, shugaba Trump ya bayyana cewa domin ya tabbatar da abinda ya fada a cikin watan Maris mai zuwa zai aike da sakataren harakokin wajen kasar zuwa kasashen Afirka a cikin wani dogon bulaguro domin kara alakar dake tsakanin Amirka da kasashen Afirka.
Wannan wasika ta Trump na zuwa ne bayan da ya firta wasu kalaman batanci ga al'ummar wasu kasashen Afirka inda ya kira su da shara, firicin da ya sha suka da mayar da martani daga jami'an dipulomasiyar kasashen Afirka da kungiyoyin kasa da kasa.
Ko baya ga hakan, Kungiyar Tarayyar Afirka wato AU ta ki tura goron gayyata ga magabatan kasar Amirka a taron ta da za ta yi karo na 30 a hedkwatar kungiyar dake birnin Adis Ababa na kasar Ethiopia da aka fara a wannan asabar, sannan a bangare guda da dama daga cikin shugabanin Afirka sun ki ganawa da Shugaba Trump a gefen taron tattalin arziƙin duniya na birnin Davos.