-
Spain: 'Yan gudun Hijira Daga Afirka 600 Sun Tsira Daga Mutuwa
Nov 19, 2017 03:17Ma'aikatan agaji na kasar Spain ne suka sanar da ceto da 'yan gudun hijirar da suka fito daga nahiyar Afirka a gabar ruwan kasar.
-
Shahadar Imam Ridha (AS)
Nov 19, 2017 03:01A yau lahadi 30 ga watan Safar ne mabiya ahul Bait (a.s) Suke juyayin shahadar Imam Ridha, (a.s)
-
Sa'ad Hariri Ya Gana Da Shugaban Faransa, Ya Ce Zai Koma Labanon Nan Kusa
Nov 18, 2017 12:54Firayi ministan kasar Labanon da ya sanar da murabus dinsa Sa'ad Hariri ya isa birnin Paris, babban birnin kasar Faransa don ganawa da shugaban kasar Faransan Emmanuel Macron wanda ya ke shiga tsakani da nufin kiran gwamnatin Saudiyyan da ta bar Haririn ya dawo gida bayan ya sanar da murabus dinsa daga can.
-
Iran Ta Ja Kunnen Shugaban Faransa Kan Tsoma Baki Cikin Harkokin Cikin Gidanta
Nov 18, 2017 12:54Tsohon ministan harkokin wajen kasar Iran kuma babban mai ba wa Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar shawara kar harkokin waje Dakta Ali Akbar Wilayati ya shawarci shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da ya guji tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Iran musamman batun tsarin tsaron kasar.
-
Rasha Ta Sake Hana Aiwatar Da Bakar Siyasar Amurka Kan Kasar Siriya A Kwamitin Tsaron MDD
Nov 18, 2017 04:55A daidai lokacin da sojojin gwamnatin Siriya suke ci gaba da samun nasara a kan 'yan ta'adda a kasar, wasu mambobin kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya suna kokarin ganin sun maida hannun agogo baya a kasar ta Siriya.
-
An Samar Da Wani Kuduri Wanda Yake Allah Wadai Da Gwamnatin Kasar Myanmar A MDD
Nov 17, 2017 02:11Komiti na ukku a babban zauren MDD ya fitar da wani sabon kuduri wanda ya yi Allah wadai da gwamnatin kasar Myanmar kan yadda take azzabtar da musulman kasar Myanmar
-
Ma'aikatar Tsaron Amurka Pentagon Ta Bada Sanarwan Isar Karin Sojojinta 3000 A Kasar Afganistan
Nov 17, 2017 02:06Ma'aikatar tsaron kasar Amurka Pentagon ta bada sanarwa a jiya Alhamis kan cewa ta kara yawan sojointa a kasar Afganisatan har guda 3000 a cikin yan kwanakin da suka gabata.
-
Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Kasar Amurka Ya Fara Ziyarar Aiki A Kasar Sudan
Nov 16, 2017 14:05Mataimakin sakataren harkokin wajen kasar Amurka ya fara gudanar da ziyarar aiki a kasar Sudan da nufin kyautata alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
-
Iran Ta Yi Watsi Da Rahoton Hukumar Kare Hakkokin Bil'adama Ta MDD
Nov 16, 2017 02:14Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da kudurin da kwamitin Majalisar Dinkin Duniya kan hakkokin bil'adama ya fitar inda ya zargi Iran da take hakkokin bil'adama inda ta ce wadanda suka gabatar da kudurin da kuma goyon bayansa su ne manyan masu take hakkokin bil'adama da kuma daure wa ta'addanci gindi.
-
Basil: Ba Mu Da Shakku Cikin Cewa Hariri Yana Cikin Mawuyacin Hali
Nov 16, 2017 02:12Ministan harkokin wajen kasar Labanon, Gebran Bassil, ya bayyana shakkunsa dangane da halin da firayi ministan kasar Sa'ad Hariri yake ciki a kasar Saudiyya yana mai cewa ci gaba da zaman Haririn a Saudiyya ba tare da dawowa gida ba wani lamari ne mai ban mamaki da tada hankali da ke nuni da cewa lalle ba dai lafiya ba.