-
Kotun Daukaka Kara Ta Tarayya A Amurka Ta Hana Maido Da Dokar Trump Ta Hana Baki Shiga Amurka
Feb 10, 2017 02:03Shugaban Amurka Donald Trump ya sake fuskantar koma baya a kokarinsa na haramta wa 'yan wasu kasashen musulmi 7 shiga Amurkan, bayan wata kotun daukaka kara ta tarayya a Amurkan ta yi watsi da karar da ya shigar na a dawo da wannan dokar bayan ta wata kotun ta soke ta a baya.
-
Barrow: Kasar Gambiya Za Ta Ci Gaba Da Zama Cikin Kotun ICC
Feb 10, 2017 02:03Shugaban kasar Gambiya Adama Barrow ya sanar da dawowa kasar cikin kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuffukan yaki bayan da tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya janye kasar daga kotun a watannin baya.
-
Amurka Ta Kashe Wani Babban Kwamandan Al'Qaida A Syria
Feb 09, 2017 02:20Ma'aikatar tsaron Amurka ta sanar da hallaka Abou Hani al-Masri, wani babban kwamandan kungiyar Al'Qaida a wani harin sama data kai a kasar Syria.
-
Majalisar Wakilan Biritaniya Ta Amincewa Gwamnati Ficewa Daga EU
Feb 09, 2017 02:19Majalisar wakilan Burtaniya ta kada kuri'ar amincewa gwamnatin kasar aiwatar da shirinta na ficewa daga kungiyar tarayyar turai ta EU.
-
Jami'an Gwamnatin Jamus Na Ci Gaba Da Nuna Rashin Amincewa Da Siyasar Trump
Feb 08, 2017 16:52Jami'an gwamnatin kasar Jamus na ci gaba da nuna rashin amincewarsu da irin salon siyasar shgaban kasar Amurka Donald Trump.
-
Daurin Shekaru 30 A Gidan Kaso A Kan Wani Da Ya Kona Masallaci A Florida
Feb 08, 2017 16:52Wata kotu a Amurka ta yanke hukuncin daurin shekaru 30 a gidan kaso a kan wani da yakona masallaci a garin Orlando na jahar Florida.
-
Ana Bincike Gidajen Iyalan Mayakan Jihadi A Jamus
Feb 08, 2017 07:47Rahotanni daga Jamus na cewa ana gudanar da bincike a gidajen iyalan wasu mutane biyu da ake zargi da taimakawa kungiyoyi jihadi na Syria.
-
Syria Ta Yi Watsi Da Rahoton Amnesty
Feb 08, 2017 07:44Gwamantin Syria ta yi watsi da rahoton kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa wato Amnesty International mai cewa an kashe dubban mutane a Kurkukun kasar a asirce.
-
Kotu A Kasar Birtaniya Zata Gudanar Da Bincike Kan Yarjejeniyar Sayar Da Makamai Ga Kasar Saudiyya
Feb 07, 2017 12:03Kotun kolin kasar Birtaniya ta sanar da shirinta na gudanar da bincike kan yarjejeniyar da gwamnatin kasar ta kulla da masarautar Saudiyya kan cinikin makamai.
-
Majalisar Britania Ba Zata Amincewa Trump Ya Yi Jawabi A Cikin Majalisar Ba
Feb 07, 2017 02:51Shugaba majalisar dokoki kasar Britani John Bercow ya bayyana rashin amincewarsa da jawabin shugaban kasar Amurka Donal Trump a cikin majalisar dokokin kasar idan ya kawo ziyara a tsakiyar shekarar da muke ciki a kasar.`