Majalisar Wakilan Biritaniya Ta Amincewa Gwamnati Ficewa Daga EU
https://parstoday.ir/ha/news/world-i17467-majalisar_wakilan_biritaniya_ta_amincewa_gwamnati_ficewa_daga_eu
Majalisar wakilan Burtaniya ta kada kuri'ar amincewa gwamnatin kasar aiwatar da shirinta na ficewa daga kungiyar tarayyar turai ta EU.
(last modified 2018-08-22T11:29:39+00:00 )
Feb 09, 2017 05:49 UTC
  • Majalisar Wakilan Biritaniya Ta Amincewa Gwamnati Ficewa Daga EU

Majalisar wakilan Burtaniya ta kada kuri'ar amincewa gwamnatin kasar aiwatar da shirinta na ficewa daga kungiyar tarayyar turai ta EU.

Kudirin ya samu karbuwa ne da gagarimin rinjaye daga 'yan majalisun inda 494 suka amince da kudirin akan 122 da suka ki amincewa da shi.

Yanzu dai za'a mika kudirin ga najalisar dattijan kasar domin neman na ta ra'ayin.

A Karshen watan Maris ne, shugabar gwamnatin kasar Theresa May ke son fara tattaunawa a hukumance kan matakin ficewar Biritaniyar daga Tarayyar Turai.

Idan a cen baya sama da kashi 2 cikin 3 na 'yan majalisar sun nuna adawa da shirin kasar na neman ficewa daga tarayya Turai din a zaben raba gardama da aka yi a ranar 23 ga watan Yuni bara, dayawa daga cikinsu na ganin cewa lokaci yayi da ya kamata su goyi bayan zabin al'ummar kasar da suka amince da shirin da kashi 52%