-
Musulman Rohinga Kimani Dubu 65 Suka Yo Gudun Hijira Daga Myanmar Zuwa Bangladesh
Jan 09, 2017 14:39Majiyar majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa daga cikin watan Octoban shekarar da ta gabata zuwa karshen shekarar musulman kasar Myanmar kimani dubu 65 suka yo hijira daga kasarsu zauwa Bangladesh
-
Wakilin Musamman Na MDD Ya Ziyarci Libya
Jan 09, 2017 07:25Wakilin musamman na sakatare-janar na MDD, kana shugaban tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Libya wato UNSMIL, Mista Martin Kobler, ya isa Tripoli, fadar mulkin kasar, inda ya yi shawarwari tare da firaministan gwamnatin hadaka ta kasar Libya Fayes al-Sarraj.
-
Gwamnatin Myanmar Ta Amince A Warware Matsalar Musulmin Kasar Ta Hanyar Diflomasiyya
Jan 08, 2017 12:16Sakamakon matsin lamba da sha kakkausar ska gwamnatin Myanmar ta amince a warware matsalar musulmin kasar ta hanyar diflomasiyya.
-
Sudan Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Soke Takunkumin Da Ta Kakaba Mata
Jan 08, 2017 08:26Kasar Sudan ta yi kira ga gwamnatin Donald Trump da za a rantsar nan ba da dadewa ba da ta sake manufarta a kan kasar ta Sudan.
-
Kasar Jamus Ta Sanar Da Rufe Masallatan 'Yan Salafiyya A Kasar
Jan 08, 2017 03:07Mataimakin waziriyar kasar Jamus Sigmar Gabriel ya sanar da cewa gwamnatin kasar za ta rufe masallatan 'yan Salafiyya da suke kasar da kuma hana su ayyukan da suke gudanarwa a kasar a shirin kasar na fada da ta'addanci.
-
Shugaban Kasar Iran Ya Taya Sabon Shugaban Ghana Nana Akufo Addo Murna
Jan 07, 2017 15:40Sabon shugaban Kasar ya yi alkawalin fada da talauci.
-
Iran Ta Bukaci MDD Ta Da Ba Wa Lamarin Musulmin Myammar Muhimmanci
Jan 06, 2017 14:19Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kirayi babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da ya ba da muhimmanci ga batun mawuyacin halin da musulmin kasar Myammar suke ciki da kuma yin dukkanin abin da ya kamata wajen ganin an fitar da su daga irin wannan halin.
-
MDD Za Ta Gudanar Da Bincike Kan Danyen Aikin Da Ake Yi Wa Musulmin Myammar
Jan 06, 2017 14:18Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa ta fara gudanar da bincike dangane da musgunawa musulmin Rohinga na kasar Myammar da jami'an tsaron kasar suke yi bugu da kari kan rahotannin da suke nuni da irin cin zarafin musulmi 'yan tsiraru da mabiya addinin Budhha suke yi da suka hada da fyade, kisa, azabtarwa da sauransu.
-
Akalla Fursunoni 33 Sun Mutu A Wani Yamutsi Da Ya Barke A Kasar Brazil
Jan 06, 2017 14:15Rahotanni daga kasar Brazil sun bayyana cewar alal akalla fursunoni 33 sun mutu a wani yamutsi da ya barke a wani gidan yari da ke jihar Roraima da ke arewacin kasar, wanda shi ne irin wannan yamutsin na biyu da ya faru a kasar cikin 'yan kwanakin da suka gabata.
-
Amurka Ta Sanya Dan Ben Laden, Cikin Jerin Mayan 'Yan Ta'adda
Jan 06, 2017 07:29Amurka ta sanya sunan Hamza Ben Laden daya daga cikin 'ya yan Ben Laden a cikin jerin sunayen mayan 'yan ta'adda na duniya.