Wakilin Musamman Na MDD Ya Ziyarci Libya
Wakilin musamman na sakatare-janar na MDD, kana shugaban tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Libya wato UNSMIL, Mista Martin Kobler, ya isa Tripoli, fadar mulkin kasar, inda ya yi shawarwari tare da firaministan gwamnatin hadaka ta kasar Libya Fayes al-Sarraj.
Bangarorin biyu sun tattauna game da wasu muhimman batutuwa, ciki har da harkokin siyasar kasar, gami da kyautata yanayin zaman rayuwar al'umma.
Da yeke bayyani ga manema labarai Martin Kobler ya jaddada cewa, kamata ya yi a ba da fifiko kan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga jama'ar kasar ta Libya.
Libiya dai ta shiga rudani ne tun bayan guguwar neman sauyin data yi awan gaba da mulkin tsohon shugaban kasar mirigayi Kanar Gaddafi a cikin shekara 2011.