-
MDD Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Zaman Lafiya A DRC
Jan 05, 2017 08:27Kwamitin tsaro na MDD yayi maraba da rattaba hannu kan yarjejeniyar warware rikicin siyasar jamhuriyar Demokaradiyyar Congo tsakanin gwamnati da 'yan adawa kasar. securitycuncul
-
Syria : Hollande, Ya Bukaci A Mutunta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta
Jan 05, 2017 08:26Shugaban kasar Faransa, François Hollande ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki kan rikicin Syria da su mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.
-
Kungiyar OIC Za Ta Gudanar Da Zama Kan Halin Da Musulmin Mayanmar Ke Ciki
Jan 04, 2017 14:20Ministocin harkkin waje na kungiyar kasashen musulmi ta OIC za ta gudanar da zaman gaggawa kan halin kunci da musulmin Rohingya suke ciki a kasar Myanmar.
-
Sabon Babban Sakataren MDD: Majalisar Dinkin Duniya Tana Fuskantar Babbar Kalubale
Jan 04, 2017 02:24Sabon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa ko shakka babu Majalisar Dinkin Duniyan tana fuskantar babban kalubale a gabanta sakamakon gazawar da ta yi wajen magance matsaloli daban-daban da suka addabi duniya.
-
Majalisar Turkiyya Ta Sake Tsawaitar Wa'adin Dokar Ta Bacin Da Aka Sanya A Kasar
Jan 04, 2017 02:23Majalisar Dokokin kasar Turkiyya ta amince da kara wa'adin dokar ta bacin da aka sanya a kasar tun bayan juyin mulkin sojin da bai yi nasara a kasar ba a watan Yulin da ya gabata, zuwa watanni uku masu zuwa.
-
Trump: Ba Za'a Sake Sakin Wani Fursuna Daga Gidan Yarin Guantanamo Ba
Jan 04, 2017 02:23Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya sanar da adawarsa ga rufe gidan yarin nan na Guantanamo yana mai cewa ba za a sake sakin wani fursuna daga gidan yarin da Amurka take tsare da fursunonin da take zargi da ayyukan ta'addanci ba.
-
Mutane 16 Ne Suka Mutu Sanadiyyar Faduwar Wani Jirgin Soje Na Kasar Venezuela
Jan 03, 2017 04:19Mutane 16 ne aka tabbatar da mutuwarsu a lokacinda wani jirgin sojen kasar Venezuela mai saukar ungulu yayi a jiya Litinin.
-
'Yan Sanda Za Su Gudanar Da Tambayoyi Wa Netanyahu Saboda Zargin Rashawa Da Ake Masa
Jan 02, 2017 14:24Rahotanni daga haramtacciyar kasar Isra'ila sun tabbatar da cewa 'yan sanda za su gudanar da wasu tambayoyi wa firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ilan Benjamin Netanyahu saboda zargin rashawa da cin hanci da ake masa.
-
Akalla Mutane 60 Sun Rasa Rayukansu Saboda Wata Tarzoma Da Ta Barke A Gidan Yarin Brazil
Jan 02, 2017 14:24Kimanin mutane 60 sun rasa rayukansu sakamakon wata mummunar tarzoma da ta barke a wani gidan yari a kasar Brazil bayan wani rikici da ya barke tsakanin kungiyoyin masu fataucin muggan kwayoyi guda biyu da ba sa ga maciji da junansu da ake tsare da su a gidan yarin na garin Manaus
-
Taro Kan Addinin Muslunci A Babban Dakin Karatu Na Chaleston A Amurka
Jan 02, 2017 10:28Babban dakin karatu na garin Charleston a jahar Carolina ta kudu a kasar Amurka zai dauki nauyin wani zama domin tattauna lamurra da suka shafi muslunci.