-
Assad: Harin Bangarori Uku Kan Siriya Zalunci Da Wuce Gona Da Iri Ne
Apr 15, 2018 12:53Shugaban kasar Siriya, Bashar al-Assad, ya bayyana cewar harin da Amurka ta jagoranta kan kasar Siriya wani wuce gona da iri ne da kuma zalunci ne a fili kan wata 'yantacciyar kasar yana mai jaddda cewar kasar Siriya ba ta da masana'antar kera makamai masu guba.
-
Kasashen Yankin Laten Amurka Sun Yi Allahwadai Da Hare-Haren Amurka, Faransa Da Britania A Kan Kasar Syria
Apr 15, 2018 02:06Kasashen Laten Amurka da dama sun nuna damuwarsu da hare-haren wuce gona da iri wadanda kasashen Amurka, Faransa da Britania suka kaiwa kasar Sirya a safiyar jiya Asabar.
-
Kwamitin Tsaron MDD Ya Gudanar Da Zaman Gaggawa Kan Harin Da Aka Kai Syria
Apr 14, 2018 13:52Kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya gudanar da zaman gaggawa a yau, domin tattauna harin da kasashen Amurka da Birtaniya gami da Faransa suka kaddamar a kan Syria.
-
Al'ummomin Duniya Na Yin Allawadai Da Harin Amurka Birtaniya Faransa A Kan Syria
Apr 14, 2018 13:51Al'ummomin duniya suna ci gaba da yin Allawadai da harin wuce gona da iri da kasashen Amurka, Birtaniya da Faransa suka kaddamar a kan Syria bisa da'awar yin amfani da makamai masu guba, ba tare da wata hujja da ta ginu kan wani bincike ba.
-
Saktare Janar Na MDD Ya Mayar Da Martani Kan Harin Da Aka Kai A Siriya
Apr 14, 2018 08:06Saktare janar na MDD ya bukaci dukkanin kasashe da su kuji yin gaban kansu da kuma aiwatar da abinda zai kara tsananta rikici a Siriya.
-
Rasha:Manufar Kai Hari Siriya Hana Binciken Kan Gaskiyar Kai Hari Da Makamai Mai Guda
Apr 14, 2018 08:06Shugaban kwamitin alaka kasa da kasa na Rasha ya bayyana cewa hare-haren da aka kai siriya taka dokokin kasa da kasa ce kuma manufarsa hana gudanar da bincike kan gaskiyr da'awar da kasar Amurka ta yi na kai hari da makami mai guba a kasar ta Siriya
-
Amurka, Faransa Da Birtaniya Sun Kai Wa Siriya Hari
Apr 14, 2018 01:59Kasashen Amurka da Birtaniya da kuma Faransa, sun kai wa kasar Siriya harin soji a cikin daren jiya Juma'a wayewar safiyar wannan Asabar, kan abunda suka kira maida martani a kan shugaba Bashar Al'Asad na Siriya bisa zarginsa da amfani da makami mai guba a yankin Duma dake kusa da birnin Damascos a ranar 7 ga watan nan.
-
Harin Siriya : Tabas Akwai Abunda Zai Biyo Baya _ Rasha
Apr 14, 2018 01:57Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce kawancen Amurka da Faransa da kuma Birtaniya ya harba makamai masu linzami sama da dari a kan kasar Siriya, saidai an kakkabo dayewa daga cikinsu.
-
Alkawulan Gwamnatin Myanmar Ga Musulmi Yan Gudun Hijira Kasar A Bangladesh
Apr 13, 2018 02:18Ministan walwala da jin dadin jama'a na kasar Myanmar ya ziyarci sansanonin yan gudun hijirar kasar da ke kan iyakar kasar da kasar Bangladesh, inda ya gana da wakilan yan gudun hijiran kimani 50 ya kuma shaida masu cewa batun kowarsu zuwa gida na daga cikin muhimman lamuran da gwamnatin kasarsa ta sa a gaba. Ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Myanmar tana duba batun basu takardun zama yan kasa.
-
Rasha: Akwai Yiyuwar Yaki Ya Barke Tsakanin Rasha Da Amurka Kan Siriya
Apr 13, 2018 01:20Jakadan kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Vassily Nebenzia, ya kirayi Amurka da kawayenta da su yi watsi da barazanar da suke yi na kai harin soji kan kasar Siriya, yana mai cewa ba zai kore yiyuwar faruwar yaki tsakanin kasar Rasha da Amurka idan har ta kai wa Siriya hari ba.