Sep 13, 2016 15:48 UTC
  • Kiyaye fadawa cikin Shubuha

shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira

Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,Shirin na Yau zai yi bayyani kan dabi'ar kiyaye fadawa cikin shubuha watau  karyar da tayi kama da gaskiya ma'ana ya kasance duk abinda mutum  zai yi na akida ne kuma aiki a kwai yardar Allah madaukakin sarki a cikin sa, amma kafin shiga cikin shirin ga wannan.

Musuc****************

Masu saurare, Hakika Alkur'ani mai tsarki ya yi umarni da dabi'antuwa da wannan dabi'a mai albarka, a yayin da yake jan hankulanmu wajen kiyaye bin son zuciya da kuma abin ke sanya kokonto a zukata ko rikitar wa wajen fassarar Ayoyin Alkur'ani mai tsarki domin bin son zukata, a cikin Suratu Ali Imrana, Allah tabarka wata'ala ya ce:(Shi ne Wanda Ya saukar  da Littafi a gare ka, akwai ayoyi bayyanannu a cikinsa, su ne tushen Littafin, akwai kuma wasu (ayoyin) masu rikitarwa (suna da wuyar ganewa).Amma wadanda suke da karkata a cikin zukatansu, sai su rika bin abin da yake rikitar daga cikinsa, don neman fitina, don kuma neman su yi masa tawili. Babu kuma wanda ya san tawilinsa sai Allah,Masu zurfi a cikin ilimi kuma suna cewa Mun bada gaskiya da shi, dukkaninsa daga Ubangijinmu yake, kuma babu mai wa'anzutuwa (da shi ) sai ma'abota hankula) suratu Ali Imrana Aya ta 7. Masu saurare wannan Aya mai Albarka ta bayyana mana halayen masu neman sanya kokonto da rikitarwa a cikin addini domin su a kulun suna bin Ayoyin da suke da shubuha ko kuma rikitarwa kuma ba sa komawa ga Ayoyin da za su fahimtar da su ma'anar wadannan Ayoyi da suke a bayyane da kuma ma'abuta ilimi domin samun tawilin su da kuma fahimtar abinda Allah tabaraka wa ta'ala yake nufi , domin bin son rai sai sun dinga fassara Ayoyin da kansu, suna karkatar da kalamar Allah tabaraka wa ta'ala bisa son zuciyarsu.

Masu saurare, Hakika dangane da dabi'ar tsoron fadawa cikin shubuha ko kuma rikitarwa na fassarar Hukunce hukuncen Ubangiji da kuma koma wajen Allah madaukakin sarki da Ma'aikin sa gami da khalifofinsa amincin Allah ya tabbata a garesu, domin sanin fahimta ma'anarsu da kuma manufar Allah madaukakin sarki,a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce (Halali a bayyane yake, hamun ma a bayyane yake, haka zalika shubuha ko kuma abinda ke rikitarwa shima a bayyane yake, duk wanda ya bar  shubuha ko kuma abinda ke da rikitarwa  ya tsira daga aiyukan sabo, kuma duk wanda ya zabi bin shubuha ya aikata sabo  ya kuma hallaka ta hanyar da bai sani ba, hakika tsayawa a kan shubuha ko kuma abinda ke rikitarwa shine mafi alheri da fadawa cikin hallaka) kuma hakika hadisai da dama sun bayyana mana cewa dabi'antuwa da wannan dabi'a mai albarka na daga cikin mahiman alamomin riko da hakikakin Addini, a cikin Littafin Tuhuful-Ukul, an ruwaito hadisi daga shugabanmu shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib(a.s) ya ce:(Asalin Addini shi ne tsayawa a kan abinda yake na shubuha ko kuma mai rikitarwa) Masu saurare bayyanar wannan dabi'a shi ne mayar da hukunce hukunce masu rikitarwa zuwa ga manba'I ko kuma tushan wahayi domin yaye rikitarwar, Shugabanmu Imam Bakir (a.s) cikin riwayar da ake ruwaito a Littafin Amaly na shekh Tusy ya ce:( duk abinda ya zo daga gare mu, wato duk abinda aka ruwaito daga garemu, idan kun same shi ya yi daidai da Alkur'ani mai tsarki to ku rike shi, idan kuma kuka same bai yi muwafaka ko daidai da Nasin Kur'ani ba ku yi watsai da shi, wanda kuma ya rikitar da ku ku mayar da shi a gare mu  domin muyi muku sharhinsa ko mu fassara muku shi domin ku fahimci abinda muke nufi).

Musuc**********************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, dabi'antuwa da dabi'ar kiyaye  fadawa cikin hukuncin dake rikitarwa na daga cikin mabi martaba na tsoron Allah tabarka wa ta'ala a cikin Littafin Hidayatul-A'imma Ila Ahakamil-A'imma, an ruwaito hadisi daga shugaban mumunai Aliyu bn Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce: (babu tsoron Allah kamar tsayawa kan ababen dake rikitarwa) a cikin Littafin Khisal an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(wanda ya fi kowa tsoron Allah daga cikin Mutane shi ne wanda ya tsaya a kan abinda ke rikitarwa, wanda ya fi kowa bauta daga cikin Mutane kuma ,shine wanda ke tsaida farilai, wanda kuma ya fi kowa Zuhdu ko kuma kudun Duniya shi ne wanda ya bar abinda yake haramun ne, wanda ya fi kowa Ijtihadi ko kokari a cikin Mutane shi ne wanda ya bar aikata zunubai) masu saurare, abinda ake nufi da dabi'antuwa da wannan dabi'a shi ne Mutum ya kiyaye fadawa cikin karyar da a zahiri  tayi kama da gaskiya , wato kadda ya aikata wani aiki har sai ya tabbatar da amintarsa daga duk wani bilbidi na Haramun ko da kuma ya kasance a zahiri yana kama da Gaskiya, ya zo cikin Littafin Nahjul-Balaga, Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib(a.s) ya ce(dalilin da ya sanya  aka kira  abinda ke da rikitarwa da Shubuha  domin yana kama da gaskiya, to saidai  su Waliyan Allah Haskensu  shi ne Yakini ko tabbaci kuma dalilinsu karkata zuwa shiriya, amma makiya Allah kiransu shi ne Bata, kuma dalilinsu a kwai makabta daga ganin gaskiya), Hakika dabi'antuwa da dabi'ar tsoron fadawa cikin Shubuha ya naga martabar Mutum zuwa samun rabauta da soyayyar  Allah madaukakin sarki, kuma bin dabi'ar shubuha ya na kai ga hasara mabayyana ranar Alkiyama, a cikin Tafsirul Burhan, an ruwaito hadisi inda a cikin sa aka tambayi Shugabanmu Imam Bakir (a.s) dangane da ma'anar wannan Aya mai albarka (wadanda kuma suka yi mummunan aiki, to sakamakon mummunan aiki irinsa ne, kuma wulakanci zai lullube su, ba su da wani mai kare su daga (azabar) Allah, kamar dai an lullube huskokinsu ne da wani yanki na dare mai duhu kirin. Wadannan su ne 'yan wuta, masu dawwama ne a cikinta) suratu Yunusa Aya ta 27, sai Imam (a.s) ya ce wadancan su ne ahalin bidi'a da shubuha Allah zai bakanta fuskarsu ranar haduwa da shi). Hakika Hadisai da dama sun yi galgadi da kaucewa Shubuha wato karyar dake kama da gaskiya domin hakan ya kan jan Mutum zuwa aikata sabon Allah wanda daga bisani zai kaisa zuwa ga hallaka, daga cikin wasiyoyin Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) da aka ruwaito cikin Littafin Nahjul Balaga, Imam (a.s) na cewa (Ina galgadinka da fadawa cikin shubuha gami da bin zuciya domin wadannan ababe guda biyu su kan jan mutun zuwa ga fadawa cikin Haram, da kuma aikata sabon Allah).

***************************Musuc*************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.