Kokarin wajen Neman Falalar Allah
shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,Shirin na yau zai yi bayyani kan dabi'ar kokari wajen nema daga falalar Allah madaukakin sarki da kuma wadatuwa daga abinda ke hanun Mutane domin yin hakan na daga cikin kyawawen dabi'un musulinci, amma kafin mu shiga cikin shirin bari mu saurari tanadin da aka yi mana a kan faifai.
***********************Musuc************************
Masu saurare, shirin na Yau zai fara da Littafin Allah madaukakin sarki wato Alkur'ani mai tsarki, a cikin Suratu Juma'a Aya ta 10 Allah madaukakin sarki ya ce:(Sannan idan aka idar da Salla, sai ku bazu a cikin, ku kuma nemi falalar Allah, ku kuma ambaci ambaci da yawa don ko kwa rabauta) wannan Aya ta bayyana cewa kasuwanci da kuma nema daga falalar Allah madaukakin sarki ya kamata ya kasance tare da ambaton Allah,da kuma hakan ya kumshi ambatonsa wajen kiyaye halal da haram.kadda kuma Mutum ya bari neman dukiya ya shagalartar da shi da tsaida sallah a farkon lokacinta da kuma sauren aiki na alheri.idan Mutum ya kiyeye wadannan ababe nemansa sai ya kasance daga cikin mafi fifikon ibadu.a cikin Littafin Man La Yahduruhul-Fakih, Shekh Saduk (r.a) ya ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) yayin da yake fassara wannan Aya mai Albarka ((Su) Mazaje ne wadanda kasuwanci da saye da sayarwa bas a shagaltar da su daga ambaton Allah da kuma tsai da salla da ba da zakka, suna tsoron ranar da zukata da idanduna suke raurawa) suratu Nuri Aya ta 37.sai Imam (a.s) ya ce sun kasance 'yan kasuwar wadanda da zarar lokacin salla yayi za su bar saye da sayarwa su gaggauta amsa kirar ubangiji wato su gaggauta zuwa ga salla, wadannan sune suka rabauta da babban sakamakon da ya fi abinda suka kasuwancinsa.
Kuma daga cikin girman Albarkar dake tattare da neman falalar Allah ba tare da shagaltuwa daga Ambaton Allah ba, rabuta da soyayyar Allah,Hakika cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce :(Hakika Allah madaukakin sarki ya na kaunar mutuman da yak ware wajen neman halal dinsa), Amirumumunin Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(Hakika Allah madaukakin sarki yana kauna ya ga bawabsa yana shan wahala wajen neman halal).
kamar yadda daga cikin albarkar dake tattare da wannan dabi'a mai girma, rabauta da sa'adar Lahira da kuma yardar Allah madaukakin sarki, a cikin Littafin Kafi, an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce:(duk wanda ya nemi Duniyarsa ta hanyar Halal,ya kame daga tambayar hallitu, ya kuma wadatar da iyalaansa, ya tausaya makobtansa, zai hadu da Allah madaukakin sarki fuskarsa tana haskawa kamar watan daren Badar wato watan da ya kamala haskensa ranar 14 ko 15.) har ila yau neman falalar Allah tare da wadatuwa daga tambaya ko roko, zai a bashi ladan mai jihadi saboda Allah, Imam Sadik (a.s) ya ce:(Idan ya kasance Mutum yana cikin kangi, wato bashi da wadata sosai, kuma yay I aiki da daidai abinda yake samu wajen ciyar da kansa da Iyalansa, ba ya kuma biyar haram, to shi kamar mujahidin ne ko kuma mai yaki ne saboda Allah).har ila yau cikin Littafin kafi, an ruwaito hadisi daga Amiri mumunin Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(Allah madaukakin sarki ya yiwa Annabi Dawuda (a.s) wahayi yace masa Ya Dawuda Hakika kai Bawa ne abin yawo badan kana ci daga baitul mal ba, baka kuma aiki ko kadan da hanunka, sai Annabi Dawud (a.s) yay i kuka har kwanaki 40, sai Allah madaukakin sarki ya yi masa wahayi na yayi amfani da karfe wajen neman halal dinsa sai ya kasance ko wata rana yana kera Garkuwa ya kuma sayar da ita dirhami 100 sai ya wadatu daga dukiyar baitul-mal), a cikin Littafin Man La Yahduruhul fakih daga cikin tafarkin Shugaban mu imam Kazim (a.s) daya daga cikin sahabansa mai suna Aliyu bn Abi Hamza y ace:( na ga babban hasan (a.s) yana aiki a cikin gonarsa har zufa ta kai ga diga-digan kakafuwansa, sai na ce fansar kaina a gareku , ina mabiya suke kuke aiki da kanku, sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa Aiki da hannuna shi ne mafi alheri gareni, kuma dukkanin ma'aifana har manzon Allah amincin Allah ya tabbata a garesu sun yi aiki da hanuwansu, kuma wannan shi ne aiki Annabawa, Mursalai da Salihan Bayi).
*********************************Musuc**********************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaba shirin zai yi bayyani kan dabi'ar hakuri na jinkirin arziki, hakika cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Muhamad Bakir(a.s) y ace:(Ma'aikin Allah (s.a.w) a Hajjinsa ta karshe da ake kira Hijjatul wada'a ya ce mala'ika Jibrilu yayi mani wahayin cewa babu wata rai da za ta mutu face ta kamala cin arzikinta, ku ji tsoron Allah wajen neman arzikinku, kada wani abu ya sanya ku, ku nemi arzikinku ta hanyar sabon Allah,hakika Allah madaukakin sarki ya raba arziki a tsakanin halitunsa ta hanyar halal bai raba shi ba ta hanyar sabonsa, duk wanda ya ji tsoron Allah ya kuma yi hakuri Allah zai basa arzikinsa ta hanyar halal,wanda kuma ya keta hurumi ya bi ta bayan bage ya kuma yi gaggawa ya dauka ba ta hanyar halal ba,za a rake masa arzikinsa na halal kuma a yi masa hasabi ranar Alkiyama) masu saurare wannan hadisi mai albarka ya bayyana mana ma'anar Hakuri wajen zuwan arziki ko kuma jinkirinsa shine Bawa ya kyautata aikinsa wajen neman arzikinsa ba tare da yayi jinkiri wajen nemansa ba ta hanyar da bai dace ba kamar karya ko magudi da makamatansu da hakan yak an janyo fishin ubangiji. Wannan bas hi ke nuna cewa mu kasala wajen neman arzikinmu bisa dogaro da wani arziki da aka sanya a gaba, wannan shi ne abinda Nassosi da dama suka yi hani kansa, misali a cikin Littafin Man La Yahduruhul Fakih an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) yayin da ya tambayi daya daga cikin sahabansa kan abinda Umar bn Muslim ya aikata? Wato shima Umar bn Muslim din Sahabin Imam ne sai aka cewa ya rungumi ibada ya bar Kasuwanci, sai Imam (a.s) ya ce kai consa, ba san cewa ba wand aba ya nema ba a karbar Addu'arsa ba, wasu Mutane daga cikin Sahaban Manzon Allah (s.a.w) yayin da wannan Aya ta sauka (Duk wanda ya ji tsoron Allah zai sanya masa mafita, Ya kuma arzuta shi, ta inda ba ya tsammani) suratu Tallaki karshen Aya ta 2 da farkon Aya ta 3, sai suka rufe kofofinsu sannan suka rumgumi Ibada suna masu cewa hakan ya isar mana.sai wannan Labari ya riski Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sai ya tura aka kira su, sai Ma'aikin Allah ya tambayesu a kan dalilin da ya sanya suka dauki wannan mataki, sai suka ce Ya Ma'aikin Allah, Allah Madaukakin sarki ya dauki nauyin arziinmu mu kuma sai muka rungumi bauta masa kawai,sai Ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce duk wanda ya aikata wannan ba za a karbi ibadarsa ba, domin haka nah ore ku da Nema, hakika ina kyamar Mutuman da zai zauna ba ya aikin komai kuma yana kira Allah ya arzuta shi, alhali ya bar neman.
Masu saurare, Hakika an ruwaito hadisai da dama wadanda suke suka kan mutanan da ba kokari wajen neman arzukinsu sai dai su dinga ci ga zufar Mutane, a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce:(La'ancecce ne wanda zai dogara rayuwarsa gaba daya a kan Mutane ma'ana wanda ba ya nema, komai yana jira a yi masa ), har ila yau an ruwaito wani Hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya tambayi wani mutum sai aka ce masa ya hadu da jarrabawar talauci, sai ya tambaya to yanzu mi yake yi? Sai aka ce masa yana gida babu abinda yake face bautar Ubangijinsa, sai ya tambaya daga ina yake samun abincinsa, sai aka ce 'yan uwansa ne suke taimaka masa, sai Imam (a.s) ya ce wallahi wadanda suke taimaka masa da abinci sun fi shi bauta) da fatan Allah madaukakin sarki ya tsare mu da mutuwar zuciya har ta kaimu ga meka hanu a wajen waninmu muna jira shi ne zai biya mana bukatun mu na yau da kulun.
***************************Musuc*************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.