Adalici wajen Neman riba
shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, Shirin na Yau zai yi bayyani kan adalci wajen neman riba, wato nisantar zalintar Mutane wajen karbar riba mai yawa a wajensu a yayin mu'amala, kafin mu shiga shirin ga wannan.
*****************************Musuc**************************
Masu saurare, shirin zai fara da Littafin Kafi na sikatu Islam Kulaini (R.t) inda a cikin sa aka ruwaito hadisi daga Abi Ja'afar Fazari ya ce:( Imam Sadik (a.s) ya kira daya daga cikin Bayinsa mai suna Musadif sai ya bashi Dirhami dubu ya ce masa ka riki wadannan kudade a matsayin Jari ka sayi kayayyaki da su wadanda za ka kai Madina domin samun ribe ta yadda za mu kula da al'amuran gida domin iyalansa sun yawaita) ma'ana Imam (a.s) ya baiwa Bawansa Jari domin ya yi kasuwanci ta yadda zai iya biyan bukatun iyalansa, kuma wannan na daga cikin kyawawen dabi'un da Allah madaukakin sarki yake so, ladansa kuma kamar ladin mai Jihadi ko kuma muce mai yaki saboda Allah ne, domin a cikinsa a kwai kamun kai da kuma wadatuwa daga abinda ke hanun mutane. Wanda ya rawito hadisin ya ce sai babban Abdullahi (a.s) ya shirya Bawansa Musadif na kayan kasuwanci shi kuma ya kama hanyar garin Masar tare da 'yan kasuwa, a yayin da suke kai hanya su suka hadu da wasu 'yan kasuwar da suka fito daga garin Masar, sai suka tambaye su kan abinda suke dauke da shi na Kasuwanci daga Madina, sai suka bayyana musu, ya yi daidai abinda ake tsananin bukata ne a garin Masar, domin irin kayansu sun kare ana nemansu ruwa jallo a garin Masar, sai 'yan kasuwar daga cikin su har Musadif bawan Imam suka yi shawarar nan take a kan sukawa kayansu kudi wato a kan ko wani abinda ake sayar da shi dinari guda su sayar da shi dinari biyu. Haka ya kasance masu saurare, haka ya kasance wadannan 'yan kasuwa suka isa garin Masar suka sayar da wadannan kaya da tsada suka ci kazamar riba kamar yadda suka yanke shawara a baya,saboda kayan da suke dauke da shi ya yanke a garin na Masar, To a nan minene matsayin Imam Sadik (a.s) a kan wannan zaramar riba da suka ci? Wanda ya ruwaito wannan hadisi sai ya ci gaba da cewa a yayin da suka tattara kudaden su, suka koma Madina, sai Musadif ya shiga wajen Imam Sadik (a.s) na dauke da jakar kudi guda biyu kowacce a kwai dinari dubu a cikin ta? Sai ya cewa Iman (a.s) fansar kaina a gareku wannan shine uwar kudin, wannan kuma ita ce ribar, sai Imam (a.s) yace masa ribar tayi yaya amma ta yaya kuka sayar da kayen? Sai Musadif ya fadawa masa yadda al'amarin ya kasance a garin Masar da kuma irin shawarar da suka yi, sai Imam (a.s) ya ce:(subhanallah, ta yaya za ku hada kai a kan wannan kazamar riba, a kan musulmin, kan ko wani dinari ku ci ribar dinare guda? Sai Imam (a.s) ya dauki jikar gudin guda, y ace wannan shine uwar gudina kuma ban a bukatar irin wannan kazamar riba sannan ya ce Ya Musadif Yaki da takobi ya fi sauki a kan neman halal).
********************Musuc*****************************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai bayyani kan dabi'ar tsatseni wajen tattance mai tsarki daga arziki, ma'ana ya kasance abinda Bawa zai ci mai halal ne mai tsarki, da babu wani harmun ko shubuha a cikinsa, Allah tabaraka wa ta'ala na cewa (Ya Ku Manzanni, Ku ci daga halal,kuma ku yi aiki nagari, hakika ni ina sane da abin da kuke aikatatawa) suratu Muminuna Aya ta 51wannan Aya mai albarka na nuni da cewa wannan dabi'a, dabi'a ce irin ta Annabawan Allah, a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga Ahmad bn Muhamad bn Abi Nasr ya ce:(Na cewa Babban Hasan Imam Ridha (a.s) Na fansar da kaina a gareka, Ka rokamini Allah madaukakin sarki da ya arzuta ni da Halali, sai Imam (a.s) ya ce masa shin ka san ko mi ake nufi da halali? Sai ya ce Na fansar da kaina a gareka abinda ke wajenmu mu nemi tsarkakekke.sai Imam ya ce: Aliyu bn Husain (a.s) ya kasance yana fadar cewa Halali abincin zababbu ne).a gefe guda kuma Nassosi da dama sun yi galgadi da cin haramun da tsawatarwa mai tsanani, a yayin da wanda ya fi kowa gaskiya canze ke cewa (Hakika Wadanda suke cin Dukiyar marayu da zalinci suna cin wuta ne kawai a cikin cukunansu, da sannu kuwa za su shiga (wutar) sa'ira.) suratu Nisa'I Aya ta 10.
Masu Saurare dabi'antuwa da dabi'ar tsantseni wajen cin abinda yake halali yana yi sanadiyar hasken zukata da hasken Allah, da rabauta da hikima wacce duk wanda aka baiwa an bashi Alheri mai yawa,A cikin Littafin Mahajjatul-baida'I fi tahzibil-Ahya'I, an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka yana cewa:(duk wanda ya ci halali kwanaki 40, Allah zai haskaka masa zuciyarsa ya kuma gudanar da hikima daga zuciyarsa zuwa harshensa,ya kuma ya sanya shi daga cikin masu gudun Duniya) domin haka ne ma neman halali ya kasance daga mafi fifikon ibada, Hakilka, a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce Ma'aikin Allah (s.a.w) Ibada kaso 70 ce mafi fifiko daga ciki shi ne Neman Halali), abin fahimta cikin wadannan Nassosi masu albarka dangane da dabi'antuwa da dabi'ar tsantseni wajen neman da Mutum zai yi ya kasance halali ne, na daga cikin hanyoyin dake sanya Bawa ya hadu da taimakon Allah, a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) daga cikin wasiyoyinsa da ya yi Mumunai ya ce (Na hore ku da tsoron Allah madaukakin sarki, da kuma za ku bukata daga wajen Allah, Hakika wallaki ba ma umartar da ku da wani abu face abinda muke umartar kawunanmu da shi,na horeku da kokari da kuma Ijtihadi, kuma idan kuka sallaci Assubahi, ku gagguta neman arzuki kuma ke nemi halali, hakika Allah madaukakin sarki zai arzutaku da halali kuma ya taimake ku a kan hakan).har ila yau (a.s) ya ce:(Idan mutum ya nemi kudansa ba ta hanyar halali ba, ya tafi aiki hajji da shi, yayin da ya cewa na amsa maka ya Ubangiji sai ace masa ba za a amsa maka ba za a karba maka ba, idan kuma Bawa ya yi amfani da Dukiyarsa ta Halal, ya kuma tafi Hajji sai a amsa masa kuma a karba masa) har ila yau wani Hadisin na cewa (tara dukiyar haramun tana bayyana a Zuriya wato ana ganin mumunan tasirin ta a cikin 'ya'ya ko kuma zuriyar wanda ya tara ta) har ila Yau hadisin na daban Imam Kazim (a.s) ya ce:( Haramun ba ta toho, ko da kuwa ta yi tohon ba za a albarkace ta ba, idan kuma aka infaki, kauta, ko sadaka a cikin ta babu lada, duk kuma abinda shi wanda ya tara dukiyar ta Haramun ya bari zai kasance masa kuziri na shiga wuta).
*******************************Musuc********************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.