Wanzar da Sallama
shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, shirin na Yau zai yi bayyani ne kan dabi'ar wanzar da sallama ko kuma yawan sallama a tsakanin Al'umma kamar yadda musulinci ya ruwaito tare da ruhin Aminci da soyayya, amma kafin shiga shirin bari mu saurarin tanadin da aka yi mana a kan faifai.
Musuc*********************
Masu Saurare, Hakika Nassosi da dama sun kwadaitar da mu da wannan kyakkyawar dabi'a, A cikin Alkur'ani mai girma Allah tabaraka wa ta'ala na cewa:(Idan kuma aka gai da ku da wata gaisuwa to sai ku amsa da wadda ta fi ta kyau ko kuma ku mayar da irinta.Hakika Allah ya kasance Mai sakantawa ne a bisa komai) suratu Nisa'I Aya ta 86, A cikin Suratu Nur, Aya ta 61ta bayyana cewa dabi'antuwa da wannan dabi'a mai girma na daga cikin dalilan dake sanya wanzuwar albarka Ubangiji ta shafi kowa da komai, Allah madaukakin sarki ya ce:(idan za ku shiga gidaje sai ku yi wa junanku sallama,(wannan) gaisuwa ce daga wurin Allah mai albarka tsattsarka.kamar haka Allah yake bayyana muku ayoyi don ku hankalta) suratu Nur karshen Aya ta 61, a cikin tafsirin Aliyu bn Ibrahim Alkummy, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Muhamad Albakir (a.s) ya ce:(idan wani Mutum daga cikin ku ya shiga Gida, idan ya kasance a kwai Mutune a cikinsa yayi musu sallama, idan kuma babu kowa cikinsa sai ya ce Aminci ya tabbata a garemu daga wajen Ubangijinmu), kuma Hakika hadisai da dama na iyalan gidan Annabta amincin Allah ya tabbata a gare su sun yi mana albishir da Lada mai girma da Allah madaukakin sarki ya yi tanadi ga wadanda suka dabi'antu da dabi'ar wanzar da sallama.Hakika cikin litattafan Amaly na shekh saduk da Ma'anil Akhlak , daga masoyinmu shugaban Manzani amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka,an ruwaito hadisi inda a cikin sa ya ce:(Hakika a cikin Aljanna a kwai wani Daki ana ganin zahirinsa daga badininsa, da kuma badininsa daga zahirinsa, wanda zai rabauta da wannan Daki daga cikin Al'umma ta shi ne mai kyakkyawan lafazi , mai ciyar da abinci domin Allah, mai kuma watsa sallama a tsakanin mutane, da kuma mai yi sallar Dare a yayin da Mutane ke kwana) sannan kuma sai Imam Sadik (a.s) ya bayyana mana ma'anar watsa sallama a tsakanin mutane bayan wannan hadisi, sai ya ce(wanzar da sallama shi ne kada ka yi rowar sallama ga ko wani mutum daga cikin musulmai) har ila yau daga cikin mahimancin dabi'ar wanzar da sallama taimakawa wajen cimma kyakkyawar dabi'ar tawari'u watau kankantar da kai kamar yadda Shugabanmu Imam Sadik (a.s) yake cewa:(daga cikin Tawari'u, ka yiwa duk wanda ka hadu da shi sallama) a wani hadisin na daban kuma shugaban Mursalai Muhamadu Dan Abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidan sa tsarkaka ya shiryar da mu cewa tasirin dabi'ar wanzar da sallama bai takaita kawai a nan Duniya ba har ma da lahira, A cikin Littafin Amaly na shekh Mufid, an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah (s.a.w) ya cewa daya daga cikin sahabansa (Ya Anas ka yi sallama ga duk wanda ka hadu da shi, sai Allah tabaraka wa ta'ala yayi maka kari a cikin kyawawen aiyukanka, ka yi sallama wanda ga Ahlin gidanka sai Allah ya yi maka kari a cikin albarkar da ya yi maka).
Musuc*************************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, hakika karin albarka na daga cikin tasiri mai girma na watsa sallama a tsakanin musulmai, kamar yadda Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya bayyana a hadisin da aka ruwaito cikin littafin Khisal na Shekh Saduk (ka kyautata alwalka sai ka fice a kan siradi kamar ficewar gilgije, ka kuma watsa sallama sai albarkar dake gidanka ta karu, ka yawaita yin sadaka cikin sirri domin ita tana kawar da fishin Ubangiji madaukakin sarki), a cikin Tafsirin Qummy na Shekh Aliyu bn Abi Ibrahim an ruwaito wani hadisi daga Ma'aikin Allah (s.a.w) wanda yake bayyana mana cewa sallamar musulmi irin sallamar 'yan aljanna ce , Sahaban Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka sun kasance idan suka je wajen sa sai su ce masa ka Ni'imtu da safe ko kuma idan da yamma ne sai suce masa ka ni'inmu da yamma wannan gaisuwa ta kasance ana yin ta ne tun a lokacin Jahiliya watau kafin zuwan musulinci, sai Allah tabarka wa ta'ala ya saukar da wannan Aya:(Idan kuma suka zo wurinka sai su gaishe ka da abinda Allah bai gaishe ka da shi ba,) suratu Mujadala wani bangare na Aya ta 8, sai Ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce hakika Allah ya canza masa da gaisuwa wacce ta fi wannan, ita ce gaisuwar 'yan Aljanna:Amincin Allah ya tabbata a gareku).A cikin Littafin Gayat, an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka yace wa sahabansa (shin kuna son in baku labarin mafi fifikon kyawawen dabi'u na ahalin Duniya da Lahira? sai suka ce Na'am ya Ma'aikin Allah, sai ya ce watsa sallama a Duniya…Hakika wanda ya fi kowa kusanci daga cikin Mutane a wajen Allah da Ma'aikinsa, wanda ya fa yiwa Dan Uwansa sallama da farko ).babban malamin nan Masanin Allah Shekh bn Fahad Alhilly cikin littafin Iddatu Da'i(عدة الداعي) ya nakalto kaolin Annabin Rahama tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce (wanda ya fi kowa rowa , wanda ya yi rowar sallama, wanda ya fi kowa rowa daga cikin mutane, mutuman da zai hadu da Musulmi bai yi masa sallama ba). Hakika Masu saurare, dabi'antuwa da wannan dabi'a mai girma na daga cikin koyi da tawaru'I na Annabi Muhamudu (s.a.w), hakika cikin littafin Amaly saduk an ruwaito hadisi daga shugaban halittu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(ababe guda biyar ba zan bar su ba har lokacin da zan bar Duniya, daga cikin su ya Ambato yin sallama ga kananen Yara, domin ya kasance sunna ko kuma abin koyi a baya Na).har ila yau a cikin Littafin Almahasin, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce:(Hakika Allah yana son masu ciyar da abinci da masu watsa sallama).ba boyayye ba ne gareku Masu saurare, dabi'antuwa da wannan dabi'a shi ne wanda ya fara gaisuwar, Hakika cikin littafin Jami'ul Akhbar, an ruwaito hadisi shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(Wanda ya fara yin Sallama ga Mutane shi ne wanda ya fi a wajen Allah da kuma Ma'aikinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka),har ila yau an ruwaito Hadisi daga Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce:(Sallama nada Lada 70, 69 na wanda ya fara sallamar ne, lada daya kuma na wanda ya amsa sallamar ne), a bayyane yake Masu saurare, abinda Imam yake nufi ga wanda ya mayar da sallamar , wanda ya maida makamarciyarta, amma idan yayi kari a kan wanda aka yi masa shakka babu zai samu lada fiye da daya.
*******************************Musuc********************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.