Sep 25, 2016 05:07 UTC

shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira

Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,a shirin da ya gabata mun yi bayyani kan dabi'ar kiyaye fadawa cikin shubuha wato karyar da tayi kama da gaskiya domin mahimancin wannan maudi'I, shirin na Yau zai ci gaba da shi, amma kafin nan bari mu saurari wannan.

Musuc***************************************

Masu saurare, Hakika daga cikin misdakin wannan dabi'a, kaucewa bin da zuciya ke rayawa Mutune bisa aikin da babu yardar Allah madaukakin sarki, inda za gaka cewa zuciya tana rayawa Mutun aikata wani aiki na karya wanda yake kama da na gaskiya, dangane da wannan ma'ana Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) a yayin da ya ga Shahararen sahabin nan Amar bn Yasir (Y T G) tare da Mugira bn Shu'uba  suna jayayya a kan wata shubuha wato karyar da take kama da  gaskiya shi kuma mugira ya dage a kanta, sai Imam (a.s) ya ce (gyale shi Ya Amar, domin shi Mugira babu abinda ya dauka daga Addini face abida zai kusantar da shi a daudar Duniya, kuma da gagam ya sanyawa kansa wannan riga kuma hakan zai sanya dalili na faduwarsa). Masu saurare bisa abinda ya gabata za mu fahimci cewa dabi'antuwa da dabi'ar tsoron ciga cikin shubuha na daga cikin tsira daga Kaidin Shaidani da masoyansa, kamar yadda aka ruwaito a cikin Littafin Hidayatul Umma fi Ahkamil-A'imma inda a cikin sa aka bayyana cewa Imam Ridha (a.s) ya fadawa wasu batattu ce (hakika wadancan Mutane ne da Shadani ya like musu, ya sanya musu shubuha a cikin Al'amuransu, kuma suna bukatar shiriya daga kawunansu, ya kasance kuma wajibi ne a gare su da su tsaya a kan abinda yake rikitarwa a gare su daga cikin abinda suka Jahilta na abinda ake ruwaito daga wajen malimansu , Hakika Allah madaukakin sarki na cewa (Idan kuma wani labari ya zo musu na aminci(cikin Nasara) sun su watsa shi,(don su raunana zukatan mumunai). Da dai za su komar da shi (watsa labaran) zuwa ga Manzo  ko kuma zuwa ga masu hankali daga cikinsu,lallai da wadanda suke tace shi (labarin) daga cikin su sun gane shi (labarin da ya kamata su watsa) suratu Nisa'I Aya ta 83.sai Imam (a.s) y ace wadanda akew nufi dac masu hanalin sune iyalan Gidan Manzin Allah (s.a.w) su ne suke tace Alku'ani kuma suka san Halali da Haramun).

Masu saurare wannan hadisi  ya bayana mana cewa shiriyar Alkur'ani mai tsarki gami da ta iyalan gidan Annabta  hanya ce na dabi'antuwa da dabi'ar kariya na fadawa cikin shubuha da kuma da tsira daga Shaidani da kaidinsa.a wani hadisi na daban kuma Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya fadawa Sahabisa Malik bn Ashtar cewa (Ya Malik Ka zabi mafi saukin Hukunci a tsakanin Mutane wanda ba zai kuntata musu Al'amura ba, ka dakatar da su a kan Al'amura masu rikitarwa wato karyar dake kama da gaskiya kuma ka basu hakuri a kan yayewar Al'amura), wannan hadisi yana  bayyana cewa dabi'ar tsoron fadawa cikin shubuha na daga cikin mafi fifikon shugabanci.har ila yau daga cikin wasoyoyin da yayi wa Dansa Imam Hasan mujtaba (a.s), Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(Ya Kai Dana kadda kafi abinda ba ka da sani a kansa, kadda ka bi hanyar da kake tsoron a kwai bata a cikin ta, domin kin bin hanyar da ake tsoron bata ya fi alheri da fadawa cikin matsala, kuma ka bar dukkanin abu da zai jefa ka cikin Rikitarwa) har ila yau cikin Littafin Guraru Hikam Imam Ali (a.s) yayi albishir ga masu wannan dabi'a mai Albarka yana mai cewa (Mallaka ga wanda rikitarwa ta Al'amura ba ta shafe shi ba).

Musuc*****************************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani kan dabi'ar taka tsantsan wajen daukan matsaya a kan wani Al'amari, duk irin matsayar da Bawa zai dauka ta kasance bisa sani da kuma Basira kadda ta kasance bisa zato da kuma gaggauwa, da kuma barin Al'amuran da suke da rikitarwa saboda tsoron fadawa cikin haramun, Nassosi na dama sun yi ishara dangane da wannan batu, A cikin Suratu hujurati Aya ta 12 Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Ya Ku wadanda kuka bada gaskiya ku nesanci mafi yawan zato, Hakika shashen zato laifi ne kadda kuma ku rika binciken laifi  kadda shashinku ya rika yi da shashi.Yanzu dayanku ya so ya ci naman dan uwansa matacce da sai kuka  ki shi,ku kuma ji tsoron Allah,hakika Allah mai karbar tuba ne mai rahama ne) masu saurare abin fahimta a wannan Aya mai girma, da farko dabi'ar taka tsantsan  na daga cikin misdakin tsoron Allah, kuma daga cikin misdakin dabi'ar takatsantsan barin yawan zato domin wani shashin zato laifi ne, ma'ana an bukaci mumuni da ya nisanci yawan zato, domin yin takatsatsan na fadawa cikin sabo. Masu saurare, daga cikin misdakin taka tsantsan a cikin Addini , tsayuwa ga Al'amuran da su keda rikitarwa wato duk al'amuran da Mutum ba shi da tabbaci wajen ingancinsa to a wannan guri, tsayuwa shine zai sanya ya tsira daga fadawa cikin hallaka, kamar yadda Hadisin shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya shiryar da mu  a cikin hadisin da aka ruwaito a cikin Littafin Almahasin, Imam (a.s) ya ce:( tsayuwa a kan ababen dake rikitarwa ya fi alheri ga fadawa cikin hallaka) har ila yau cikin wannan Littafi, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Bakir (a.s)  ya ce :(Da Bayin Allah za su tsaya a al'amuran da ba su da masaniya cikinsa, da ba su fadawa cikin Damuwa da kafirci ba) har ila yau daga cikin misdakin wannan dabi'a, abinda Shugabanmu Annabin Rahama Muhamadu Dan Abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya shiryar da mu inda ya ce:(duk wanda ya aikata wani aiki ba a kan sani ba, barnarsa ta fi gyaransa yawa). Kamar yadda daga cikin misdakin dabi'antuwa da wannan dabi'a ta taka tsantsan komawa zuwa ga wadanda Allah madaukakin sarki ya sanya su makoma na sanin gaskiya da kuma daukanta, wato Alkur'ani mai girma, da kuma iyalan gidan Annabta tsarkaka, hakika cikin Littafin Almahasin an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) na cewa (duk wanda fahimci gaskiya daga cikin Alkur'ani mai girma ba, ba zai tsira daga fitintinu ba) har ila yau Imam (a.s) ya ce (kadda ku yi kokarin fassara abinda ba ku sani ba daga cikin abinda ya sauka a gare ku ku tsaya a kansa ku koma wajen shugabanin musulmi domin sun sanar da ku gaskiya kuma su dora ku a kan mahanga kamar yadda Allah madaukakin sarki ya ce( sai ku tambayi ma'abota ilimi idan ya zamana ba ku sani ba) suratu Nahali Aya ta 43.

***************************Musuc*************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.