Oct 05, 2016 14:10 UTC

, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira

Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, a shirin da ya gabata mun yi  bayyani kan dabi'ar wanzar da sallama ko kuma yawan sallama a tsakanin Al'umma kamar yadda musulinci ya ruwaito tare da ruhin Aminci da soyayya,  shirin na Yau kuwa zai yi bayyani kan dabi'ar gaisuwa hanu da hanu domin shi ma na daga cikin kyawawen dabi'un da Allah madaukakin sarki ke so,amma kafin shiga shirin bari mu saurarin wannan.

Musuc*********************

Masu Saurare,shirin na Yau zai fara da hadisin da shekh Mufid ya ruwaito cikin litattafansa na Amaly da kuma shekh Kuleni cikin Littafinsa Alkafi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(idan kuka hadu kuyi haduwa cikin aminci da sallama ta hanu da hanu, idan za ku rabu kuma , ku rabu cikin a yiwa juna gafara) mailman hadisi  sun ce wannan hadisi ya shafi musulmi da ma makiya idan aka hadu da su a gaisa a ba juna hanu kuma idan za a rabu ya kamata ya kasance a yi rabuwa cikin yafewa juna, saidai wani hadisin na daban ya karfafa wannan dabi'a mai kyau gad an uwanka Mumuni, Hakika cikin Littafin Khisal daga Kofar Ilimin Muhamadiya wasiyinsa yardadden Allah, Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce( idan kuka hadu da 'yan uwanku ku gisa hanu da hanu ku bayyana musu jin dadinku ta hanyar murmushi, idan kuka rabu cikin wani yanayi na murna duk wani zunubi dake kanku an karkare muku shi) har ila yau a wani hadisin na daban Imam(a.s) y ace:(ka bawa makiyinka hannu ku gaisa ko da kuwa ya ki, domin wannan shi ne Umarnin Allah madaukakin sarki a yayin da yake cewa:( To ka ingije mummuna da abin da ya fi kyau, yayin nan sai ka ga wanda yake tsakaninsa da kai gaba ce ya zamanto kamar wani masoyi ne na kusa* Ba ko wanda ake bai wa (wannan dabi'ar) sai wadanda suka yi hakuri, ba kuma wanda ake bai wa ita sai mai babban rabo) sutaru Fussilat daga Aya ta 34 zuwa ta 35, a bayyane yake istidlalin da Imam (a.s) ya yi da wannan Aya mai albarka shi ke nuna cewa dabi'antuwa da wannan dabi'a mai albarka nada tasiri babba wajen karya lagon gaba da kuma wanzar da soyayya a tsakanin Mutane.Masu saurare, a cikin Littafin Sawabul-A'amal na shekh Saduk an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) wanda yake shiryar da mu girman dabi'ar gaisuwa ta hanu da hanu inda yake cewa:(ku da gaisuwarku hanu da hanu ladanta kamar ladan wadanda suka yi yaki saboda Allah ne) har ila yau wannan dabi'a mai girma na janyo girman rahamar Ubangiji  kamar yadda shugabanmu Imam Bakir (a.s) yayi ishara cikin hadisin da aka ruwaito a Littafin Kafi na sikatu islam kulaini, Imam (a.s) ya ce:(Hakika idan mumunai suka hadu suka kuma yi gaisuwa hanu da hanu, Allah tabaraka wa ta'ala zai sanya albarka a tsakanin hanayensu sannan zai ya fuskanci fuskar wanda ya fi nuna kauna da soyayya ga Dan uwansa , idan kuma Allah ya fuskance da rahamarsa sai su karu da zunubansu kamar yadda ganyan itace suke rabuwa da itace a yayin da suka bushe), har ila yau cikin Littafin Mahasin an ruwaito hadisi daga Shgabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce ( hakika a yayin mumunai suka hadu kowanne daga cikin ya gisa hanu da hanu tare da Dan uwansa, Allah tabaraka wa ta'ala ba zai kushe ba yana dibin su da Soyayya da kuma gafararsa, kuma Hakika za a kankare musu zunubansu har lokacin da suka rabu), Masu saurare tasirin wannan musafaha ya shafi dukkanin Musulmai kamar yadda Kaulin Imam Bakir (a.s) ya yi ishara da shi a hadisin da aka ruwaito cikin Littafin Kafi (babu wani musulmi da zai hadu da Dan uwansa musulmi ya gaisa da shi hanu da hanu , Yatsotsin suka hadu da juna, zai zunuban dake gare su sun rabu da su, kamar yadda ganyen itace ke zuba a lokacin bazara). Masu saurare dabi'antuwa da wannan dabi'a na daga cikin misdakin daukan dabi'un Mala'ikun Allah amincin Allah su tabbata a garesu,kamar yadda Sadikul-Amin amincin Allah ya tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka cikin hadisin da aka ruwaito cikin Littafin Kafi (gaisuwa hanu da hanu  da Mumuni ya fi gaisuwa hanu da hanu da Mala'ika).

Musuc*****************************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani dangane da wani bangaren hadisai da suke bayyani kan mahimancin gaisuwa hanu da hanu ko da kuwa a yayin da mutane za su rabu na dan kankanen lokaci,a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Muhamad Bakir (a.s) ya ce:(ya kamata ga Mumunai idan dayansu zai rabu da dan uwansa koda da kewayen itaciya ne idan suka sake haduwa gaisawa hanu da hanu a tsakaninsu).wannan al'amari kalilan na daga cikin Sunar Annabi Muhamadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka kamar yadda Hadisin da aka ruwaito cikin Littafin Kafi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce (Musulmi sun kasance idan suka tafi yaki tare Ma'aikin Allah (s.w.a),sannan idan suka fice daga wani wuri mai rukukin itace watau mai yawan ita ce suka kuma fita daga wannan wuri sai ko wane ya dibi dan uwansa su gaisa hanu da hanu).wasu hadisan kuma sun bayyana cewa duk mutuman da za ku gaisa da shi kadda ka yi saukin janye hanunka har sai shi da kansa ya bukacin hakan domin yin koyi da sunar Ma'aikin Allah (s.a.w).a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce:(Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka bai taba gaisawa hanu da hanu da wani Mutum ba ya janye hanunsa daga hanun mutuman har sai shi da kanshi ya janye hanunsa daga Hanun Ma'aikin Allah), har ila yau a wani hadisin na daban Shugabanmu Imam Bakir  (a.s) ya yi mana albishir da girman ladan dake tattare da wanda yayi koyi da sunar Ma'aikin Allah ta hanyar wannan dabi'a,inda yake cewa:(Idan Mutum ya gaisa hanu da hanu da Dan uwansa, wanda ya fara ya karbi gaisuwa ya fi yawan lada da wanda ya bayar, saidai a yayin da hanunsu ke hade juna zunuban da suka aikata zai kushe har sai ya kasance ba su da zunubi ko daya).Masu saurare, a wani hadisin na daban kuma Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya bayyana tasirin wannan dabi'a mai albarka na kore mumunar dabi'a ta rike mutum ko kuma abikin fada a zuci, a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(ku gaisa hanu da hanu a tsakanin ku domin yin hakan na gusar da mumanar dabi'ar na rike mutum ko abokin fada a zuci).a wani riwaya da Muhamad bn Makki Al'amuly wanda ake kira da shahidin farko ya ruwaito cikin Littafin Arba'in daga Ibn Bastam ya ce:(na kasance a wajen babban Abdullahi Imam Sadik (a.s) sai wani Mutum ya shiga ya ce fansar kaina a gareka ya Dan Ma'aikin Allah ni daga mutanan Jabal ne, kuma a yayin da na hadu da Dan uwana sai na rungume shi domin jin dadin haduwarmu da shi, sai wasu Mutane suke aibata ni suna cewa wannan dabi'un baki ne ba larabawa ba da kuma ahlin shirka, sai Imam Sadik (a.s) ya ce minene dalilinsu da fadar hakan domin Ma'aikin Allah (s.a.w) ya rungumi Dan uwansa Ja'afaru Tayyar kuma ya sunbaci tsakanin idanunsa)

Musuc*******************************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.