Oct 09, 2016 09:26 UTC

shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira

Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,Shirin na yau zai yi bayyani ne kan mahimancin giramama Marayu tare da tausaya musu domin yin hakan na daga cikin kyawawen dabi'un da Allah madaukakin sarki ke so sannan ya yiwa mai wannan dabi'a kyakkyawan sakamako da Lada mai dunbun yawa, amma kafin shiga shirin, bari mu saurari tanadin da aka yi mana kan faifai.

*******************************Musuc*****************************

Masu saurare, Hakika dabi'ar girmama marayu na daga cikin mafi girma da kuma albarka na kyawawen dabi'un musulimci dake yin sanadiyar rabauta da samun kusanci a fadar Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka a cikin Aljanna madaukakiya,wannan shi ne abinda Masoyin Allah Mustapha (s.a.w) ya yi bishara da shi, cikin riwayar da aka ruwaito cikin littafin Kurbur Isnad ya ce:(duk wanda ya reni Marayya ya ciyar da shi zan kasance ni da shi a Aljanna kamar haka, wato Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya nuna yatsotsin sa masu albarka manuniya da kuma ta tsakiya ya kamar haka za mu kasance tare a cikin Aljanna) a cikin Litattafan Khisal, Almahasin da Sawabul A'amal, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce:(ababe hudu duk wanda ya kasance a cikin su Allah madaukakin sarki zai gina masa gida Aljanna, duk wanda ya shayar da Maraya, ya yi rahama ga mai rauni,  mai biyayya ga iyaye, mai kuma tausayin ga wadanda suke kalkashin sa). Hakika shakka babu albarkar dake tattare da girmama Marayu ta shafi Duniya da Lahira, A cikin Littafin Amaly na shekh Saduk, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) na cewa:(duk wanda yake son Allah tabaraka wa ta'ala ya sanya shi cikin rahamarsa, ya kuma zaunar da shi a Aljanarsa to ya kautata dabi'unsa, ya girmama Maraya, ya kuma taimakawa Bako, kuma ya kaskantar da kai ya yi wadu'I ga Allah n da ya halice shi), wasu hadisan kuma sun bayyana cewa Albarkar da mai girmama Maraya zai samu ba za ta tsaya  a kansa kawai ba za ta shafi har ma'aifansa bayan rasuwarsu,Hakika cikin Littafin Amaly Saduk  an ruwaito hadisi daga Annabin Rahama, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:( Annabi Isa (a.s) ya na ficewa sai ya bi ta kan wani kabari sai tarar ana yiwa wanda ke cikin Kabarin azaba, wata shekara da ta zagayo  sai ya sake bi ta wannan kabarin, sai ya tarar a wannan shekarar ba a yiwa wanda ke cikin kabarin azaba ba, sai ya ce  Ya Ubangiji a shekarar da ta gabata ta bi ta wannan kabari na tarar  ana azabar da wanda ke cikin wannan kabari, sai kuma a wannan shekarar na samu cewa ba a azabatar da wanda ke cikin kabarin ba, sai Allah madaukakin sarki ya yi wahayi a gare shi: ya ce Ya Ruhun Allah shi wannan Mutum ya nada Da Salihi ya kautata hanyar sa ya kuma shayar da marayu sai na yi masa gafara saboda aikin da Dansa ya aikata) kamar yadda dabi'antuwa da wannan dabi'a mai girma ke yin sanadiyar rabauta da hasken zuciya, Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(Babu wani Bawa da zai shafi kan Maraya domin tausayinsa sai Allah madaukakin sarki ya bashi haske ranar Alkiyama adadin gashin da ya shafa na wannan maraya). Har ila yau Ma'aikin Allah (s.a.w) ya shiryar da mu da dabi'antuwa da dabi'ar rahama ga maraya da cewa na daga cikin hanyoyin da suka magance kumci da kuma kakkausar zuciya, a cikin Littafin Sawabul A'amal an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce (Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce duk wanda yake gudun samun kaushin zuciya daga cikin ku, to ya dauki Maraya ya tausayasa masa ya kuma rungume shi ya shafi kansa sai  zuciyarsa ta yi  taushi da Allah madaukakin sarki ).

*********************Musuc*******************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani kan dabi'ar shaglatuwar mumuni ga gyaran aibinsa maimakon ya shagalto da kalon aibin waninsa.A cikin Littafin Khisal, an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka y ace(aibin Mutum ya ishe shi da ya nemi sani aibin Mutane alhali jahilci nasa aibin, yana kuma kunyar su da abinda shi kan sa ya nada shi, kuma ya cutar da abokin zaman sa a kan abinda ba shafe shi) kamar yadda Ma'aikin Allah (s.a.w) ya yiwa sahabinsa Abu zaril Gaffari (yardar Allah ta tabbata a gare shi) wasiya na ya dabi'antu da wannan dabi'ar gyara kai a maimakon wasu Mutane da suke shagaltuwa da laifin Mutane ya ce Ya Aba Zar kadda ya cutar da kai abinda Mutane suke aikata wa alhaki kai ma ba ka sani ba kai ma kana iya aikata irinsa nan gaba) watau ya Aba zar kadda ka yi fishi da mutane domin sun aikata wani aiki mummuna alhali kai ma nan gab aba ka sani ko hakan za ta fari a kanka. Har ila yau cikin Littafin Amaly na shekh Saduk an ruwaito wani hadisi na daban daga fiyeyyen halitta tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(mafi saukin alkheri wajen samun Lada shi ne biyayya, kuma mafi saukin shari wajen samun mumanan sakamako shi ne Alfahasha,ya isa ga Mutum da ya basirantu daga aibin Mutane, da aibin da ya kasa ganewa kansa) watau ya kamata Mutane idan ya fahimci aibin Mutane to ya dubi kansa shin shi ma yana aikata wannan mumunan aiki, idan yana yi ya gyara, a memakon ya shagalto da Mutane.

Masu saurare,Hakika daga cikin mafi girman amsa wasiya da kuma Shiriyar Muhammadiya,juyawa da kuma Jihadin Mutum wajen gyara kansa har ta kai ga cimma kamala na tsakaka daga duk wani aibi, kamar yadda Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya yi ishara cikin hadisin da aka ruwaito cikin Littatafan Khisal,Almahasin da sauransu, inda ya yi ishara na biyu zuwa ga Son Allah madaukakin sarki ga masu wannan dabi'a inda zai sanya su a kalkshin inuwarsa, Imam (a.s) ya ce:( Mutane uku za su kasance cikin inuwar Allah madaukakin sarki Ranar da babu wata Inuwa sai ta shi, Mutuman da ya yi wa Mutane adalci daga kansa, da Mutuman da bai fifita wani mutum ba ko kuma ya kaskantar da shi har sai ya san hukunci Allah madaukakin sarki a kan sa, Yarda ko kuma fishi, da kuma Mutuman da bai aibata wani Mutum ba ko kuma ya bata shi saboda wani aibi da yake da shi har sai yayi kokarin gyara aibinsa domin babu yadda za a yi Mutum ya kore wani aibi zai wani aibin na daban ya bayyana a gare shi) masu saurare hakika daga mahimancin wannan dabi'a shi ne wasiyar da shugaban Mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya yiwa Dansa Imam Husan (a.s) cikin riwayar da aka ruwaito cikin Littafin Tuhuful Ukul, ya ce (Ya Kai Dana duk wanda yake kalon aibi ko laifin kansa ya shagaltu daga aibi ko laifin waninsa) har ila yau kamar yadda ya zo cikin Tafsiru Aliyu bn Ibrahim Kummy yayin da yake bayyana kan kyakkyawar makoma ga masu wannan dabi'a, Amiru Mumuni (a.s) ya ce:( Albarka ta tabbata ga wanda ya shagaltu ga aibi ko laifukanka a maimakon kalon na Mutane).

************************Musuc**********************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.