Kare Mutane Daga Cutuwa
Shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,Shirin na yau zai yi bayyani ne kan daya daga cikin kyawawen dabi'un musulinci da Allah madaukakin sarki yake girmama masu irin wannan dabi'a ya kuma basu sabati a kan ta tare da kyakkyawan sakamako, wannan dabi'a kuwa it ace dabi'ar kare Mutane daga cutuwa.amma kafin shiga cikin shirin bari mu saurari wannan.
************************Musuc*****************************
Masu saurare, shirin na yau zai fara da Littafin Adda'awat na Sayid Jalil salihin bawan nan Kutubu din Rawandi,inda a cikin sa aka ruwaito wani hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce wajibi ne ga ko wani musulmi ya yi sadaka a ko wata rana, sai aka ce wa nene ya wajabta hakan ya Ma'aikin Allah?sai Ma'aikin Allah (S.A.W) hidimar ka na kare cutuwar mutane a kan hanyar su sakana ne, (watau idan Mutum ya ga wani abu da zai cutar da Mutane a kan hanya ya kawar da shi sadaka ne),nunawa Mutune hanya sadaka ne, gaida maras lafiya sadaka ne,umarninka da kyakkyawa sadaka ne, amsa sallama ma sadaka ne) Masu saurare daga cikin wadannan ababe da aka Ambato kawar da abinda zai cutar da musulmi daga hanya na da baban ladar da ya kai na karatu Alkur'ani mai girma, Hakika cikin Littafi Amaly na Shekh Tusy an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(duk wanda ya kawar da abinda zai cutar da musulmi daga hanyar su, Allah zai rubuta masa ladan wanda ya karanta Ayoyi arba'in na Alkur'ani mai girma da a cikin ko wani harafi za a bashi lada goma) , har ila yau dabi'antuwa da wannan dabi'a na daga cikin hanyoyi masu albarka dake sanya mai su ya rabauta da gidan Aljanna, Hakika cikin Littafin Alkhisal, an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce:(Bawa zai shiga Aljanna a dalilin ya kawar da wata kaya da ta kasance a kan hanyar musulmi ya dauke ta domin kadda ta cutar da su) har ila yau masu saurare, daga cikin mafi girma na misdakin dakile abinda zai cutar da musulmai shi ne, taimakon Mabukata, masu rauni ko Nakasasu da makamantansu, a cikin Littafin Kurbatu Isnad an ruwaito hadisi daga Annabin Rahama Muhamadu Dan Abdullahi tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(Allah tabaraka wa ta'ala ya yiwa Annabi Dawud (a.s) wahayin cewa Ya Dawud Hakika Bawa zai zo mini da wani aiki mai kyau ranar Alkiyama sai in yi masa hukunci da gidan Aljanna, wato in saka masa da gidan Aljanna, sai Annabi Dawud (a.s) ya tambayi ubangiji ya ce wannan wani aiki ne? sai Allah madaukakin sarki ya ce damuwar da ya kawar wa dan uwansa mumuni ko da ta kasance daidai gwalgwadon barin Dabino watau idan Bawa ya shafewa Dan uwansa hawaye cikin wata matsala da yake fuskanta ko da kuwa ta barin dabino ne, sai Annabi Dawud (a.s) ya ce Ya Ubangiji wajibi ga wanda ya sanka kadda ya yanke kauna a gareka) har ila yau an ruwaito hadisi daga Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) dangane da girman ladan dake tattare da kawar da abinda zai cutar da Mutane, Imam (a.s) ya ce:(duk wanda ya kawar da abinda zai cutar da musulmi, ruwa ne ko wuta ko kuma makiyi domin girmama muslmin Allah tabaraka wa ta'ala zai gafarta masa zunubansa) har ila yau cikin suratu Khisal an ruwaito hadisi daga masoyin Allah Mustapa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(dukkanin kyautatawa sadaka ce,kuma duk wanda ya yi nuni da wani alheri aka aikata shi, ladansa kamar wanda ya aikata shi ne, Allah kuma yana son taimakon mabukata).
*********************Musuc****************************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani kan dabi'ar wadatar zuci, watau Bawa ya wadatu da abinda ke hanun Mutane domin yin hakan na daga cikin kyawawen dabi'un musulincin da Allah madaukakin sarki ke so.a cikin tafsiru Aliyu bn Ibrahim yardar Allah ta tabbata a gare shi, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:( yayin da wannan Aya mai albarka ta sauka(Kada kuma ka zura idanuwanka ga abin da Muka jiyar da wasu daga cikinku dadi da shi , kada kuma ka yi bakin ciki da su, kuma ka kaskantar da kanka ga muminai) suratu Hijri Aya ta 88 Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(Duk wanda bai yanke kauna daga wadatuwar sa ba watau madaukakin sarki, zuciyarta ta rabu da duk wata hasarar Duniya, kuma duk wanda ya jefa idanunsa bisa abinda ke hanun waninsa, Damuwarsa za ta karu, kuma bacin ransa ba zai warke ba, duk kuma wanda bai san cewa Allah madaukakin sarki ya nada Ni'ima sai a abinci ko a sutura, to hakika aikinsa ragegge, kuma duk wanda ya wayi gari cikin bakin ciki da bacin rai, to ya wayi gari cikin fishin Allah madaukakin sarki) a cikin wannan hadisi Masoyin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya shiryar da mu dangane da yanayin dabi'un da aka ki tare kuma da hanyoyin da Mumuni ya kamata ya bi domin tsira daga tabewa kuma wannan hanya ita ce dabi'ar wadatuwa daga abinda ke hanun Mutane, domin haka ne za mu samu cewa Ma'aikin Allah (s.a.w) ya siffata mana cewa wadatar zuci ita ce mafi fifikon dabi'ar wadatuwa da abinda ke hanun Mutane, kamar cikin wani hadisi da shekh Saduk ya ruwaito cikin Littafin sa mai suna Amaly saduk daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(mafi alherin watada, wadatar zuci). Har ila yau cikin Littafin Amaly na shekh Saduk, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) inda a cikin sa yake bayyana mana albarkar da mai dabi'ar watadar zuci ke cimmawa(abu uku abin alfaharin mumuni ne kuma adonsa ne a Duniya da Lahira, Sallar karshen Dare, yanke kaunarsa daga abinda ke hanun Mutane, da kuma wulayar Imami daga cikin limaman iyalan gidan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka), Masu saurare dabi'ar wadatar zuci wasilar mumuni ce wajen rabauta da amsar Du'a'insa gami da cimma falalar Allah wacce ba ta da iyaka, hakika cikin Littafin Amay na shekh Tusy, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:( Idan dayanko yana so idan ya tamabayi Allah wani abu ya bashi, to ya yanke kauna daga wajen Mutane baki daya, kadda ya kasance ya nada fata a wajen wani face Allah madaukakin sarki, idan Allah tabaraka wa ta'ala ya san cewa Bawa ya nada wannan dabi'a har cikin zuciyarsa to babu wani da zai tambaye shi face ya bashi shi). A cikin Littafin Khisal, an ruwaito wani hadisi, inda a cikin sa aka ce wani Mutum ya je wajen Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce Ya ma'aikin Allah ka koyar da ni abinda idan na aikata shi Allah zai so ni kuma a Doron kasa na samu soyayyar mutane, sai Ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce masa ka yi kodayin abinda ke wajen Allah sai Allah madaukakin sarki ya soka, ka kuji abinda ke hanun mutane sai su soka).A cikin Littafin Fikhu Ridha (a.s) an ce wani Mutum ya je wajen Ma'aikin Allah (s.a.w) domin ya tambaye shi wani mikdari na dukiya, sai ya ji Ma'aikin Allah (s.a.w) yana cewa duk wanda ya tambaye mu za mu bashi, wanda kuma ya wadatu daga tambaya Allah zai wadatar da shi, sai wannan mutum ya tafi ba tare da ya tambaye Ma'aikin Allah wani abu ba, wata rana ya sake komawa wajen Ma'aikin Allah da wannan nufi amma sai ya ji Ma'aikin Allah yana fadar abinda ya fada a baya, an yi haka har so uku, sai ya koma ya je ya yi aron katari ya shiga daji ya saro itace ya kai kasuwa ya sayar da shi da rabin ma'auni na Sha'ir ya kai gidansa suka ci shi da iyalinsa sannan ya ci gaba da wannan sana'a ta itace har sai da ya tara gudin sayar gatari ya saye na shi na kansa sannan kuma ya mayar da na aro, a kwana a tashi, da wannan sana'a ya saye ragumma guda biyu da Bawa guda da suke aiki tare, ya zamanto mai arziki sai ya koma wajen ma'aikin Allah (s.a.w) ya bashi labarin al'amarinsa sai Ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce (shin ba na gaya maka duk wanda ya tambayemu za mu bashi, wanda kuma ya wadatu daga tambaya Allah zai wadata shi).da fatan Allah madaukakin sarki Masu Saurare ya bamu wadatar zuci ta yadda za mu kawar da idanunmu da abinda ke hanun Mutane mu zamanto masu daga hannayanmu a wajen su shi kadai don albarkar riko da waulayar iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka.
*********************Musuc***************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.