Tsoron Allah daga aikata Makirci
shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,Shirin na yau zai yi bayyani ne kan tsaron Allah a kan makirci da Yaudara domin hakan na daga cikin kyawawen dabi'un musulinci na masoyan Allah madaukakin sarki wajen gudanar da mu'amalar su tare dukkanin Mutane gaba daya, kuma wannan shine abinda Nassosi da dama suka shiryar da mu, amma kafin shiga cikin shirin ba ri mu saurari tanadin da aka yi mana a kan faifai.
*********************Musuc*******************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, Nasossi da dama sun bayyana mana cewa Makirci da yaudara na daga cikin ababen da suke kan Mutum zuwa ga mumunar makoma, tabewa tare da hasara bayananna kuma wannan na daga cikin dabi'un makiyan Allah madaukakin sarki, Allah tabarka wa ta'ala ya ce:( kuma suka shirya makirci, Mu kuma Muka shirya ruguza makircin su, alhali kuwa su ba su sani ba* Sai ka dub aka ga yadda karshen makircinsu ya zama, watau Mun hallakar da su tare da mutanensu baki daya) suratu Namli daya Aya ta 50 zuwa ta 51.A cikin suratu Fa'diri Aya ta 10 Allah madaukakin sarki ya ce:(……..Wadanda kuwa suke shriya makirci suna da (sakamakon )azaba mai tsanani,kuma makircin wadannan shi ne yake lalacewa). Har ila yau a cikin wannan Surat mai Albarka Aya ta 43 Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Don girman kai a bayan kasa da kuma makirci mummuna.(sakamakon ) makirci mummuna kuwa bay a sauka sai a kan masu shi. Ba abin da suke saurare in ban da hanyar da ta samu mutanan farko,sannan ba za ka taba samun wani canji ba game da hanyar Allah, kuma ba z aka sami wani canji ba game da hanyar Allah), Masu saurare hakika dabi'antuwar da dabi'ar tsoron Allah daga makirci gami da yaudara na daga cikin alamomin gaskiyar Imani da musulinci, kamar yadda Masoyinmu Mustapha tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya bayyana cikin hadisin da aka ruwaito cikin Littafin Uyunul Akhbaru Ridha (a.s) ya ce:(Duk wanda ya kasance musulmi ne ba ya makirici da yaudara, domin Na ji Mala'ika Jibrilu (a.s) yana cewa hakika Makirci da yaudara na cikin wuta, ba ya daga cikinmu wanda yake yiwa musulmi magudi, kuma ba ya daga cikin su wanda yake ha'intar musulmi), har ila yau Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(ba ya daga cikinmu wanda yake yiwa musulmi magudi, ko kuma yake cutar da shi ko yaudarar shi).abinda ake nufi da makirci da yaudara wadanda suke wajabta shike wuta da kuma suke karkata zuwa wayo , karya, yaudarar, magudi da makamantan sun a daga cikin munanan aiyuka, domin haka ne aka kore wadannan siffofi daga masoyan Allah, a cikin Littafin Sawabul-A'amal, an ruwaito hadisi daga Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce (in ba dan na ji Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka yana fadar cewa:Makirci, yaudara, da ha'inci dukkanin cikin wuta, da na kasance wanda ya fi kowa makirci daga cikin kabilar Larabawa)A cikin Littafin Nahjul-balaga an ruwaito hadisi daga Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce:(Na rantse da Allah Mu'awuya bai fi iya makarkashiya ba, sai dai yana yaudara kuma yana fajirci, in ban da an ki makarkashiya ba, da na kasance wanda ya fi kowa iya makarkashiya daga cikin Mutane, saidai duk wata makarkashiya fajirci ce, kuma Fajirci kafirci ne)masu saurare abin fahimta cikin wannan Nassi shi ne makirci da yaudara da abinda ya shafe su na makarkashiya suna kai mai yinsu zuwa ga fajirci da kuma kafrici kuma wannan ba dabi'un Mumunai ba ne, dabi'u ne na Kafirai da suke yi musu jagoranci zuwa wuta.a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga Asbag bn Nabatat ya ce wata Rana a bisa Minbari a birnin Kufa yayin da yake khuduba Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(Ya Ku Mutane in banda makarkashiya abin ki ce da na kasance wanda ya fi kowa iya makarkashiya daga cikin Mutane, ku saurara!Hakika duk wani nau'I na makarkashiya fajirci ne, kuma fajirci kafirci ne, Ku saurara! makarkashiya, fajirci,da ha'inci dukkaninsu wuta ce)
*************************Musuc*****************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani ne kan dabi'ar nisanta daga mumunar dabi'ar fadar munanan kalaman ga mutane ko cin mutunci da makamantansu, hakika Ayoyin Alkur'ani da dama sun bayyana irin munanan sakamako na masu wannan dabi'a kamar fishin ubangiji da kuma Azaba mai radadi.cikin Suratu Taubat Aya ta 79 Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Wadanda kuma suke aibata mumunai masu yin sadaka (mai yawa) daon neman lada da kuma wadanda kawai suke ba da (kadan)gwargwadon ikonsu, sannan su dinga yi musu izgili, to Allah ya saka musu game da izgilin, suna kuma da (sakamakon) azaba mai radadi) a cikin Littafin Uyunul-Akhbar an ruwaito wani hadisi mai tsaho inda a cikin sa a ka yi bayyani dangane da ma'anar izgilin Allah ga masu izgili, Imam Aliyu Arridha (a.s) ya ce:(Hakika Allah madaukakin sarki ba ya izgili kuma ba ya ba'a, ba ya makirci kuma ba ya yaudara, saidai shi madaukakin sarki yana sakamasu sakawar ba'a, izgili, makirci, da yaudara, Allah madaukakin sarki ya daukaka da abinda Azzalumai suke fada ya yi girma) abin fahimta a wannan hadisi mai albarka shi ne daga cikin kyawawen dabi'un musulinci,tsoron Allah daga munanan dabi'u na batanci, izgili da kuma ba'a har ma yin hakan ga masu yiwa Mutane izgilin tare kuma meka al'amarinsu zuwa ga Allah madaukakin sarki ya saka masu da kansa a kan munan aiyukan su. Dangane da musababin saukar Ayar da ta gabata, abubuwa guda biyu sun shiryar da mu dangane da wani bangare na misdakin irin Ba'a, izgili da batancin da Allah madaukakin sarki ba ya so da kuma ya kamata mu kiyaye aikata su, abu na farko riwayar da Ambato cikin Tafsiru Aliyu bn Ibrahim Alkummy, inda Rawin ya ce: (Salim bn Umair Al-Ansari ya je wajen Ma'aikin Allah (s.a.w) da sa'I guda na Dabino ya ce Ya Ma'aikin Allah na yi aiki na bayar da ruwa a wata Gonar Dabino aka bani sa'I biyu na dabino sai na dauki sa'I guda domin iyalaina wannan sa'I guda kuma na baiwa Allah rance,sai Ma'aikin Allah (s.a.w) ya bada umarni a raba a tsakanin Al'umma sadaka , sai Munafikai suka fara yi masa izgili suna cewa mun rantsa da Allah , Allah mawadaci daga wannan sa'I na dabino, Allah mai zai yi da wannan dabino nasa, saidai Aba Akil lakabi na Salim Ansari, ya so ya ambaci kansa domin a bashi daga cikin wannan sadaka sai Ayar ta sauka).Masu saurare hakika munafikai sun yi wa wannan mumuni izgili sun ce yayi hakan ne domin Ma'aikin Allah (s.a.w) ya san talaucin sa kuma ya dinga bashi sadaka, domin haka ne ma aka hana yin kokonto ga Al'amuran Mutane. Masu saurare abu na biyu kan dalilin saukar wannan Aya, hadisin da Shekh Muhamad bn Mas'oud Al-Ayyashi ya ruwaito cikin tafsirinsa daga shugabanmu Imam Ja'afaru sadik (a.s)ya ce:(Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya je wajen aiki a kan ko wani bokici guda da shayar da itacen dabino za a bashi dabino guda, bayan ya gama wannan aiki sai ya zo da dabinon da ya samu wajen Ma'aikin Allah (s.a.w) a kan a rabawa Fakirai, A bakin kofa a kwai Abdurrahaman bn Auf sai yayi masa yafice, sai wannan Aya ta sauka) da fatan Allah madaukakin sarki ya tsare mu da irin wadannan munanan aiyuka don daraja da kuma albarkar riko da wulayar iyalan gidan Annabata.
*********************Musuc***************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.