Kauracewa mumunar dabi'ar kifce da yafice
Shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,Shirin na Yau zai yi bayyani kan dabi'ar nisanta ko kuma kauracewa mumunar dabi'ar kifce da yafice, wulakanci da kuma cin mutincin Mutane, kuma ya kamata mu kauracewa batanci ga wasunmu da kuma mumunan zato tare da sanya shakku cikin kyawawen aiyukansu. kafin shiga cikin shirin bari mu saurari tanadin da aka yi mana a kan faifai.
*********************Musuc************************
Masu saurare, mai yiyuwa wannan Aya mai girma na daga cikin Ayoyi mafi tsanani da suke galgadinmu kan mumunar dabi'ar kifce da yafice, Allah madaukakin sarki ya ce:(tsananin azaba ya tabbata ga duk wani mai kifce da yafice) suratu Humazati Aya ta 1.Hakika dangane da tafsirin wannan Aya an bayyana cewa Kifce da yafice na daga cikin ababen da suke shafe matsayin Mutun zuwa matsayin dabba, a cikin Littafin Alkhisal, an ruwaito hadisi daga Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(Na tambayi Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka kan abubuwan da suke canza mutun daga siffassa ta asali sai ya ce su goma sha uku ne yana bayyani har inda ya ce ka ga yadda Mutan yake canzawa zuwa Kunama, shi ne Mutuman da ya kasance mai yafice ba ya gaishe da mutane da harshen sa har abada ba) har ila yau cikin littafin na Khisal, an ruwaito hadisi daga Imam Sadik daga Ma'aifinsa daga kakansa Imam Sajjad amincin Allah ya tabbata a gare su ya ce:(abinda ke canza siffar bani Adama 13 ne har zuwa wurin da ya ce amma ka ga Kunama, Mutuman da ya kasance mai kifce da ya fice Allah zai canza siffassa zuwa ta kunama) hakika ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya kwadaitar da mu kan tsananin kauracewa mumunar dabi'ar Kifce da yafice ta hanyar bayyana mana mumunar sakamakonsa ga wadanda suka jarabtu da wannan mumunar dabi'a.Hakika cikin Littafin Awalil Aly, da kuma tafsiru Aliyu bn Ibrahim Alkummy, an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(Daren Isra'I na ga wasu Mutane ana yanka Naman jikinsu sannan ana sanya shi a cikin Bakunansu , ana kuma ce musu kuci abinda kuka kasance kuna ci daga cikin Naman 'yan uwanku, sai Nace Ya Jibrilu su waye wadancan Mutane? Sai ya ce wadancan su ne Masu kifce da yafice daga cikin Al'ummarka), har ila yau a cikin tafsiru Aliyu bn Ibrahim Alkummy dangane da misdakin kifce da yafice an bayyana cewa ma'anar kifce shine mutuman da ya kasance yana kaskantar da tallakawa , ma'anar yafice kuma wanda yake sunkuwar da wuyansa yana fishi a duk lokacin da ya ga wani tallaka ko kuma almajiri.
Masu saurare daga cikin albarkar dake tattare da mai dabi'ar kaucewa yin kifce, yafice, ba'a ko batanci ga mutane ,shi ne cimma tabbacin bautar Allah madaukakin sarki na gaskiya, domin rashin kauracewa wadannan munanan dabi'u ya kan nisantar da Mutum hakikanin bautar Allah madaukakin sarki kamar yadda Shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya bayyana a riwayar da aka ruwaito cikin Littafin Ikabul-A'amal yana mai cewa(tir ga Bawa mai kifce da yafice ya na kalon ka da wata fuska, yana kuma baka baya da wata fuska ta daban) abin fahimta cikin wannan hadisi shi ne kifce da yafice yana jefa mai yinsu cikin nifaki, kamar yadda daga cikin mumunan tasirin su kauracewa mutane daga mai wannan mumanar dabi'a tare da mumunan zato a gare shi, wannan kuma shi ne abin shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya shiryar da mu a riwayar da aka ruwaito cikin Littafin Guraru Hikam, Imam (a.s) ya ce:(mai kifce abin zarki ne kuma mai tabo ne a tsakanin Mutane)
**************************Musuc*************************
Masu sarare ci gaban shirin zai yi bayyani ne dangane dabi'ar kyakkyawan zato ga Mutane tare kuma da kauracewa mumunan zato a gare su domin yin hakan na daga cikin hanyoyin da suke sanya hutuwar zuciya da kuma amincinta, kuma wannan na daga cikin alamomin gaskiyar imani da kuma kyakkyawar bauta ga Allah madaukakin sarki,hakika hadisan da suka gabata sun yi ishara dangane da wannan batu, wasu Nassosi na daban sun yi tabbaci a kan wannan kyakkyawar dabi'a wajen mu'amala tare da Mumunai.A cikin su Nuri Aya ta 12 Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Ina ma lokcin da kuka ji shi, mumunai Maza da mumunai Mata sun zatar wa kawunansu alheri suka kuma ce, wannan ai Kage ne bayyananne) A nan karantarwar Alkur'ani mai girma tana kiran mu da yin riko da kyakkyawan zato ga Mumunai da kuma kin gasganta abinda muka ji a kan su ba tare da wani tabbaceccen dalili ba, da babu yadda za a iya kare wa, domin yin taka tsantsan a kan yi musu kazafi, domin hakan na daga cikin manyan laifuka kamar yadda wadannan Ayoyi masu albarka suka shiryar da mu, Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Yayin da kuke bayeneneniyar sa (kagen) da harashenku, kuke fadar abin da ba ku sani ba da bakunanku,kuke kuma tsammaninsa abu ne mai sauki,alhali kuwa shi mai girma ne a wurin Allah*Ina ma da yayin da kuka ji shi, cewa kuka yi Bai dace da mu, mu yi irin wannan Magana ba "(kuma ku ce) "Subhanallahi! Ai wannan kage ne babba*Allah yana gargadin ku kadda ku koma yin irinsa har abada idan kun zamanto mumunai).Suratu Nuri daga Aya ta 15 zuwa Aya ta 17 Masu saurare Ayar karshe cikin Ayoyin da suka gabata ta ishara kan cewa kyakkyawan zato na daga cikin alamomin gaskiyar Imani ga Allah madaukakin sarki, Hakika cikin Littafin Kafi na Sikatu Islam Kulaini, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(idan Mumuni ya zarki Dan uwansa,Imani zai shafe daga cikin zuciyar sa kamar yadda Kishiri ke narkewa a cikin Ruwa) har ila yau Imam (a.s) na cewa:( Duk wanda ya zarki Dan Uwansa cikin Addininsa to babu wani sauren haramci a tsakanin su), hadisin Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya shiryar da mu kan cewa mumunan zarki ga Mumunai ya fi karya muni da hadari, hakika cikin Littafin kurbatu Isnad, an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce:(Hattara da zarki, domin shi zarki ya fi karya karya(watau shi ne babbar karya) kuma ku kasance 'yan uwa saboda Allah kamar yadda Allah ya umarce ku, kadda ku kasance masu gasa, masu bincike kan abinda shashen ku ke aikatawa, Kada sãshenku yã yi gulmar sãshe, kadda ku kasance masu jayayya, masu kiyayya da junansu , kadda ku zamanto masu hassada domin ita hasada tana cin Imani kamar yadda wuta ke cin busasun itace).Masu saurare hakika hadisai da dama sun shiryar da mu kan iltizami da dawwama a kan dabi'ar kyautata zato ga mumunai, A cikin Littafin Khisal an ruwaito hadisi daga Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce :(Mumuni ba ya ha'intar dan uwansa, ba ya kuma kaskantar da shi, kuma ba ya zarkinsa, ba ya kuma ce masa Ni na nisantu da kai.. ka nema ma Dan uwanka Uziri (kan abinda ka ji a kan sa) ku ku ji mumunan zato a tsakanin ku domin Allah madaukakin sarki ya yi hani a kan sa)
**********************Musuc*************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na