Nov 06, 2016 13:03 UTC

shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci

Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,Shirin na Yau zai yi bayyani kan Juriya da kuma riko da Addini a cikin ko wani hali, amma kafin shiga shirin ga wannan.

********************Musuc************************

Hakika Masu saurare, juriya da kuma da riko da addini cikin halin da Dan Adam ya tsinci kansa ciki na daga cikin kyawawen dabi'un musulinci kuma na daga cikin umarnin Allah tabaraka wa ta'ala ga masoyinsa Annabinsa mai girma amincin Allah ya tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka A cikin suratu Hudu Allah tabaraka wa ta'ala ya ce: (saboda haka sai ka mike sosai kamar yadda aka umarce ka kai da wadanda suka tuba tare da kai, (su ne mumunai) kada kuwa ku yi shisshigi. Hakika shi (Allah) Mai ganin abin da kuke aikatawa ne *kuma kada ku karkata zuwa ga wadanda suka yi zalinci, sai wuta ta shafe ku, ba ku kuwa da wasu mataimaka ba Allah ba, sannan ba zai taimake ku ba) suratu Hudu Aya ta 112 da kuma ta 113. A wasu Ayoyi na daban kuma Allah madaukakin sarki ya yi albishir da masu wannan kyakkyawar dabi'a tare da tabbaci na Mala'iku da kuma taimakon su a gare su da kuma kyakkyawar makoma gami da rabauta a Lahira, kamar yadda cikin suratu Fussilat, Allah madaukakin sarki ya ce:( Hakika wadanda suka ce:"Allah ne Ubangijinmu", sannan suka daidaita, to mala'iku za su sauko musu (lokacin mutuwa suna cewa) kada ku tsorota, kuma kada ku yi bakin ciki, kuma ku yi farin ciki da Aljanna wadda kuka kasance ana yi muku alkawarinta*Mu masoyanku ne a rayuwar duniya da kuma ta Lahira, kuma kuna da duk abin da rayukanku suke marmari, kuna kuma da duk abin da kuke nama) suratu fussilat Aya ta 30 da kuma ta 31, har ila yau wani Nassin kuma ya bayyana cewa dabi'antuwa da wannan kyakkyawar dabi'a na daga cikin hanyar rabauta da rai mai nutsuwa, a cikin suratu Ahkafi Aya ta 13 Allah tabaraka wa ta'ala ya ce: (Hakika wadanda suka ce Allah ne Ubangijinmu sannan suka tsaya tsayin daka to, babu tsoro a gare su kuma su ba za su yi bakin ciki ba), Hakika Masu saurare dabi'antuwa da dabi'ar juriya gami da tsayin daga kan Addini na daga cikin gaskiyar Imani da kuma tabbatuwar sa a cikin zukata, a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce:(Mumuni ya fi Dutse karfi da juriya domin shi Dutse ya na rabuwa daga Dan uwansa shi kuma Mumuni ba ya rabuwa da Addininsa ko kadan) a cikin Littafin Siffatu Shi'a na Shekh Saduk, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:(Hakika Mumuni ya fi guntattakin karafa karfi domin shi guntattakin karafa idan suka shiga wuta suka canza, shi kuma Mumuni ko da an kashe shi aka sake tayar da shi sannan kuma aka kashe shi zuciyarsa ba za ta canza ba), Masu saurare, kamar yadda daga cikin albarkatun dake tattare da dabi'antuwa da dabi'ar tsayin daga a kan gaskiya, rabauta da Addu'ar Shugabanin Shiriya iyalan gidan Annabta tsarkaka da kuma taimakon su ga Mumuni wajen samun sabati da kuma juriya tare da rabauta da kusancin su da soyayyarsu sannan kuma soyayyar Allah da yardarsa tare kuma da kyakkyawar makoma, wannan shi ne abin da Sikatu Islam kulaini cikin Littafin Alkafi ya ruwaito daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:(Hakika Hawariyan Annabi Isa (a.s) sun kasance mabiyansa,kuma mabiyanmu su ne Hawariyawan mu, bai kasance kuma mabiya da kuma mataimakan Annabi Isa (a.s) sun fi  yi masa biyayya a kan mabiyanmu, kai ku saurare wallahi ba su taimaka masa daga cutarwar yahudawa kuma ba su yi yaki bayan sa ba a kan sa , amma ka ga mabiyanmu wallahi ba su guske ba tun bayan da Allah madaukakin sarki ya dauki ran Ma'aikin sa tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka suna taimaka mana kuma suna yaki saboda mu bayan mu, suna shan tuhuma kuma ana azabtar da su, da kuma mayar da su sanuwar ware a gariruwa, Allah kuma ya saka musu da Alheri da abinda suke yi mana) da fatan Allah madaukakin sarki ya sanya mu daga zababbun mabiya iyalan gidan Annabta tsarkaka wadanda suka samu sabati da juriya bisa Addini na gaskiya domin shi mai ji ne kuma mai karbar Addu'a ne.

***********************Musuc********************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani kan dabi'ar 'yantuwa daga Son Duniya domin shi ma na daga cikin kyawawen dabi'un da Allah madaukakin sarki ke so, kuma Nassosi da dama sun yi bayyani dangane da hakan. Masu saurare abinda ake nufi da wannan dabi'a shi ne kadda Dan Adam ya shagaltu da Dadin Duniya da kuma ba shi mahimanci ta yadda zai shagaltar da shi daga rayuwar Lahira  kamar yadda fadar Allah madaukakin sarki yayin da yake siffanta tababbu  ke cewa:(Wannan kuwa saboda su sun fi son rayuwar duniya a kan ta Lahira, kuma hakika Allah ba ya shiryar da Mutane kafirai* Wadannan su ne wadanda Allah ya toshe zukatansu da jinsu da ganinsu, kuma wadannan su ne gafalallu*Ba shakka lallai su a Lahira su ne tababbu) suratu Nahli daga Aya ta 107 zuwa ta 109.Wannan Ayoyi masu girma suna ishara kan cewa Son Duniya da kuma kaskantar da kai daga kanginta na daga cikin martabobin kafirci daga Ni'imar Allah, domin shi Allah ya sanya Duniya gidan guziri da kuma tanadi na kyawawen aiyuka na gina gidan Lahira, hakika Duniya ba gidan dawwama ba ne, shagaltuwa da abinda ke cikin ta ya kan yi sanadiyar makabtar zuciya da kuma gafala da aikata aikin da zai sanya a gina rayuwa ta hakika ta ranar Lahira, har ila yau daga cikin shagaltuwa da Duniya da kuma kaskantar da kai ga kanginta shi ne Mutum ya katange kokarinsa wajen tara duk abinda yake bukata na Arzikin rayuwar Duniya, hakika cikin littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(Isa Dan Maryamu amincin Allah ya tabbata a garesu ya ce: shin kuna aiki dan Duniya alhali ana arzuta ku a cikin ta ba tare da aiki ba, ba kwa kuma aiki dan Lahira alhali ku ba a arzuta ku a cikin ta sai da aiki, ta yaya zai kasance ga ahalin ilimi da wanda ke hanyar sa zuwa ga Lahirarsa ya fuskanci Duniyar sa (watau ya rungume da hanu biyu biyu ba ya tunanin Lahira alhali kuma yana kan hanya ne na zuwa Lahira), shin abin zai cutar da shi ya fi son sa ga abinda zai amfanar da shi) daga wannan  hadisi za mu fahimci cewa daga cikin misdakin 'yantuwa daga kangin son Duniya shi ne ya kasance mumuni yana kwadayin abinda ke lahira da kuma yardar Ubangijinsa har ma wajen kokarin da aikinsa na neman abinda yake bukata na gudanar da rayuwar  Duniya  kamar ya kasance niyarsa meka kai ga umarnin Ubangiji wajen kokari na Neman arzikinsa, ba wai kawai mutum ya kasance mai kwadayin Duniya da kuma tara Dukiya. Masu saurare, daga cikin muhiman albarkar dake tattare da dabi'ar 'yantuwa daga kangin Duniya shi ne rabauta da wadata ta hakika da kuma tsarkaka daga talaucin ma'anawi, kamar yadda Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya bayyana cikin hadisin da aka ruwaito a Littafin Usulul Kafi, Imam (a.s) ya ce:( Duk wanda ya wayi gari ya kuma yini yana kalon Duniya a matsayin babban fatansa, Allah zai sanya masa talauci a idanunsa ya kuma watsa al'amuransa, ba kuma zai samu komai face abinda aka raba a nan Duniya aka bashi ba, duk kuma wanda ya wayi gari ya kuma yini, lahira ita ce babban fatansa Allah ta'ala zai sanya wadata a zukiyarsa ya kuma tattara masa Al'amuransa), a cikin wani hadisin na daban kuma Imam (a.s) ya bayyana cewa:(mafi wadata daga wadatattu shi ne wanda bai kasance ya na tsoron kangi ba, kada ku shagaltar da zukatanku kan abinda ya baku a baya, ku shirya tunaninku kan shirin da ya ke da shi a yanzu).

*********************Musuc***************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.