Dbi'ar 'yantuwa daga Kangin Duniya 2
Shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,a shirye shiryen da suka gabata mun yi bayyani kan mahimancin dabi'ar 'yantuwa daga kangi ko kuma bautar Duniya, gamin mahimancin maudi'in shirin na Yau ma zai dora daga inda muka tsaya a shirin da ya gabata, amma kafin nan bari mu saurari wannan.
*************************Musuc*******************************
Masu saurare shirin na Yau zai fara da hadisin Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) wanda yake bayyana mana mahimancin wannan kyakkyawar dabi'a na tsira daga mumunar makoma, Hakika cikin Littafin Khisal, an ruwaito hadisi daga Shugaban Mumunin Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(duk wanda ya bauta wa Duniya ya kuma fifita ta a kan Lahira zai yi mumunar makoma). Kamar yadda daga cikin albarkar dake tattare da dabi'ar 'yantuwa daga bautar Duniya, budewar Zuciya da kuma samun Nutsuwa, gami da samun buwaya da izza a Duniya da Lahira, A cikin Littafin Zuhudu na Shekh Husain bn Saeed Al-Ahwazi, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:(duk wanda ya wayi gari kuma Duniyace kawai ya sanya a gaba ,ita ce babban fatansa, Allah zai dagula Al'amuransa ya rasa kan gadonsa, kuma talaucin sa zai kasance a tsakanin idanuwansa, ba kuma zai samu komai ba daga jin dadin Duniyar sai abinda Allah madaukakin sarki ya kaddara masa, kuma duk wanda ya kasance gina gidansa na Lahira shine burinsa da babban fatansa, Allah madaukakin sarki zai ya ye masa kuncinsa, ya kuma tattara masa Al'amuransa, Duniyar za ta zo masa a matsayin kaskantarta), har ila yau Masu saurare kamar yadda daga cikin albarkar dake tattare da da wannan kyakkyawar dabi'a, rabauta da wadata ta hakika,samun hutun zuciya da kuma rashin bada mahimancin da damuwa gami da izza, wannan shi ne abinda Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya yi mana ishara da shi a wani Jami'in Hadisi dake bayanin ilolin samun Albarka daga cikin albarkatu. Hakika Shekh Saduk Rahamar Allah ta tabbata a gare shi,cikin Litattafansa uku watau, Ma'anil-Akhbar, Ilalu shara'I'I da kuma Alkhisal ya ruwaito wannan Hadisi da sanadinsa ke komawa zuwa ga Imam Sadik (a.s) ya ce:(bukatun Mutane a wannan Duniyar Kararriya guda hudu ne, Wadata, jin dadi, rajin damuwa da kuma karfi(kamar na milki da sauransu ta yadda zai nisanta daga kaskanci), amma kun ga wadata ana samun ta ne ta hanyar kana'a watau wadatar zuci, duk wanda yake naman ta a tarun Dukiya ba zai same ta ba, shi kuma jin dadi ana samun sa a cikin karancin shagaltuwa da neman Duniya da kuma jin dadinta, duk wanda ya neme ta a yawan yin yawan aiyuka domin tara dukiya da daudar Duniya ba zai same shi ba, shi kuma karfi da buwaya ana samun sa ne ta hanyar yi wa mahalicci hidima, duk wanda ya neme shi ta hanyar yiwa halittu hidima ba zai same shi ba) masu saurare abinda ake nufi da yiwa halittu hidima shi ne yi musu aiki domin samun duniya, amma idan yi wa halittu hidima dan neman yardar Allah madaukakin sarki ne shi ma yiwa mahalicci hidima ne kai yana ma daga cikin tsarkakkakun ibadu da kuma kyawawen aiyukan da ake gina gidan Lahira da su. Har ila yau daga cikin girmar albarkar dake tattare da dabi'ar yantuwa daga bautar Duniya, samun yardar Ubangiji da kuma gafararsa, a cikin Littafin Amaly na Shekh Saduk, an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(Ku saurara! Duk wanda aka baiwa zabi tsakanin Duniya da Lahira, ya zabi Duniya a kan Lahira, zai hadu da Allah ranar Alkiyama ba shi dawani kyakkyawan aiki da zai yi masa garkuwa daga shiga wuta, duk kuma wanda ya zabi Lahira a kan Duniya Allah zai yarda da shi ya kuma gafarta masa daidai gwalgwadon aikinsa). Kuma kamar yadda daga cikin albarkar dake tattare da wannan kyakkyawar dabi'a tsira da fitintunu gami da rabauta da biyan bukatu daga Ubangiji da kuma gaggauta aikata alheri, Hakika Sayyid Kutubudin Rawandi cikin littafinsa (Kisasul-Anbiya'i) ya ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:(ya kasance daga cikin kiran da Allah madaukakin sarki ya yiwa Annabinsa Musa (a.s) kadda ka karkata zuwa ga Duniya kamar yadda Azzalimai suka rungume ta, da wadanda suka karkata gare ta suka kuma rike ta a matsayin uwa da Uba, Ya Kai Musa Da zan wakilta maka kanka Da San Duniya, da adonta ya rinjayeka,Ya Musa ka aikata alheri tare ahlinsa, ka ma riga su wajen aikata alherin, ka rabu da Duniya da kuma abinda ka ke ganin wadatuwa ne na ta, kadda zuciyarka ta dinga raya maka cewa ko wani nau'in aiki an wakilta shi zuwa gare ka, ka sani ko wata fitina tsuronta shi ne Son Duniya).
**************************Musuc**************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a shafa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen hausa na muryar Jamhoriyar musulinci ta iran dake nan birnin Tehran, ci gaban shirin zai yi bayyani kan dabi'ar kakkyawar Niya, watau ya kasance duk aikin da Mutum zai yi ya sanya kakkyawar Niya a cikin sa, ma'ana ya yi niya da nufin samun kusanci da Allah madaukakin sarki a dukkanin aiyukansa, da kwadayin neman yardarsa.Ya zo cikin wasiyar Annabi Muhamadu (s.a.w.a) ga babban sahabinsa Abi Zaru Gaffary yardar Allah ta tabbata a gare shi ya ce:(Ya Aba Zar ya kasance ka sanya Niya a ko mai har wajen yin barci da kuma cin abinci) abinda ake nufi ya kasance Niyar Mumuni a ko wani aiki ta bashi karfin gwiwa wajen yin ibada da aikata aiki na gari.Masu saurare Hakika Litattafai daga bangarori biyu Shi'a da Sunna sun ruwaito wannan hadisi daga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce:(Hakika ko wani aiki sai da niya, kuma ko wani Mutum da abinda ya yi nufi) , daga bangaren iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka kuma, an ruwaito hadisi daga Kakansu Mustapa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka kamar yadda ya zo cikin Littafin Wasa'ilu Shi'a, ya ce:( Hakika ko wani aiki sai da niya, kuma ko wani Mutum da abinda ya yi nufi, duk wanda ya yi yaki da nufin kwadayin abinda ke wajen Allah hakika Ladan sa na wajen Allah madaukakin sarki, kuma duk wanda ya yi yaki domin neman Duniya ba zai samu komai ba face abinda ya yi nufi) ma'ana Niya ta alheri da kuma neman yardar Allah madaukakin sarki ita ke sanya aiyuka na gari da suke samun kyakkyawan sakamako daga wajen Allah tabaraka wa ta'ala, a cikin Littafin Almahasin, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce: (Hakika ranar Alkiyama, Allah na tayar da Mutane a kan niyar su). Masu saurare, Hadisai daga iyalan gidan Annabin Rahama amincin Allah ya tabbata a gare su sun bayyana cewa fadadar Rahamar Allah tabarka wa ta'ala ta na shafar mai kyakkyawar niya na aikin Alheri ko da kuma ba aikata shi ba, a cikin Littafin kafi an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru sadik (a.s) ya ce:(Hakika Bawa Mumuni fakiri, idan ya ce Ya Ubangiji ka arzuta ni in aikata kaza da kaza na kyawawen aiyuka da kuma na alheri, idan Allah ya tabbatar gaskiya da kyakkawar niya daga gare shi, sai ya rubuta masa Ladan da ya kamata ya rubuta masa idan ya aikata, Hakika Allah mai yalwatawa ne masani). Kuma Daga cikin albarkar dake tattare da dabi'ar kyakkyawar Niya da kuma niyar Alheri, yardar Allah madaukakin sarki na aiyukan mumuni, kamar yadda Hadisin da aka ruwaito cikin Littafin Almahasin daga Abi Basir ke cewa:(Na tambayi Babban Abdallah Imam Sadik (a.s) kan yawan Ibadar idan aka aikata zai kasance an cika hakki, (watau an biya hakin Ubangiji) sai Imam (a.s) ya ce kyakkyawar Niya wajen Da'a da biyayya).
*********************Musuc***************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.