Kyakkyawar Niya
Shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, Shirin na Yau zai yi bayyani kan dabi'ar kyakkyauwar Niya da kuma neman yardar Allah a dukkanin aiyukan da muke yi domin yin hakan na daga cikin kyakkyawar dabi'un da Allah madaukakin sarki ke so, amma kafin shiga shirin ga wawann.
*******************Musuc*******************************
Masu saurare, hakika dabi'ar kyakkyawar niya da kuma neman yardar Allah a dukkanin aiyukan da muke aikatawa na daga cikin kyawawen dabi'un da Allah madaukakin sarki ke so, daga cikin misdakin wannan dabi'a shi ne Mumuni ya yi kokarin cewa dukkanin abinda zai aikata ya kasance ya yi daidai da sunar Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, wacce Shugabanin shiriya daga Limaman iyalan gidan Annabta tsarkaka suka koyar da mu.kuma wannan,shi ne abinda ake yiwa lakabi da aiki daidai da Sunna, a cikin Littafin Kafi na sikatu Islam kulaini, an ruwaito Hadisi daga Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce:(magana ba tare da aiki ba ,ba ta da wata kima, ,kuma magaba da aiki ba su da wani tasiri sai da niya, furici, aiki da Niya kuma ba su da wani tasiri sai sun kasance bisa koyarwar Sunna), Masu saurare dabi'ar kyakkyawar Niya da gaskiyar sa wajen neman yardar Allah bisa yadda sahihiyar Sunna ta Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka za ta kasance salihar Niya wacce ta fi ma kyakkyawan aiki da kansa, kamar yadda aka yi ishara cikin Hadisin Ma'aikin Allah (s.a.w.a) da aka ruwaito cikin Littafin Almahasin , Manzon Allah(s.a.w.a) ya ce:(Niyar Mumuni ta fi alheri da aikinsa, niyar Kafiri kuma ya fi sharri ga aikinsa, shakka babu ko wani Ma'aikaci na aiki ne a kan niyarsa) ma'ana abinda ake nufi da wannan hadisi shi ne aikin mumuni zai bisa kyakkyawar niyarsa da kuma gaskiyarsa na neman yardar Allah ba wai kawai kyakkyawa a zahiri ba.Masu saurare daga cikin albarkar dake tattare da kyakkyawar niya, nemam alheri da yardar Ubangiji, fadadar arziki da kuma bunkasar sa, a cikin Littafin Khisal, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:( Duk wanda harshensa ya kasance mai gaskiya, ya tsarkake aiyukansa,duk kuma wanda ya gyra niyarsa Allah zai kara masa arzukinsa, duk kuma wanda ya kyautata biyayarsa ga iyayensa Allah zai kara masa kwanukansa a Duniya), har ila yau masu saurare daga cikin albarkar dake tattare da dabi'ar kyakkyawar niya gami da neman alheri, tsira daga rabkanuwa na samu damar gudanar da aikin da ya yi niyar aikatawa na alheri.daga cikin wasiyar da Annabin Rahama Muhamadu Dan Abdullahi (s.a.w.a) ya yi wa babban sahabinsa Abu Zarul Gaffari yardar Allah ta tabbata a gare shi wacce aka ruwaito cikin Littafin Amaly na shekh Saduk ya ce:(Ya Aba Zar ka bada himma wajen aikata kyakkyawa, ka kasance cikin kyakkyawar Niya a ko wani yanayi ko da kuma ba ka aikata su ba, hakan zai sanya ba za a rubuta ka daga cikin gafalalu ko kuma masu rabkanuwa ba), a cikin wani hadisi na daban kuma Shugaban shiriya (s.a.w.a) ya yi mana bushara da cewa Allah madaukakin sarki ba ya bari kyakkyawan fata ga bawansa har sai ya tabbatar masa da shi, a cikin Littafin Khisal, an ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce:(duk wanda ya yi fatan wani abu domin Allah da kuma neman yardarsa, ba zai bar Duniya ba har sai Allah ya bashi (watau ya ciki masa fatansa)). Kamar yadda daga cikin albarkar dake tattare da wannan dabi'a cimma ladan aikin ko da kuwa wanda yayi kyakkyawar niyar bai riski aikata aiki na alherin ba, a cikin Littafin Basa'iru-Darajat, an ruwaito hadisi daga Aliyu bn Abi Hamza, sahabi ne na Imam Musa Kazim (a.s) ya ce:(Babban hasan Musa Alkazim (a.s) ya ce min Allah ya jikan wane, watau yana nufin daya daga cikin sahabansa, Ya kai Ali ba ka halarci jana'izarsa ba? Sai na ce masa A'a hakika na son in halarci jana'izarsa, sai Imam (a.s) ya ce min hakika Allah ya rubuta maka Ladansa halartar jana'izar saboda kyakkyawar niyarka).
***********************Musuc******************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jamhoriyar musulinci ta Iran, ci gaban shirin zai kawo muku wani gungun Nassosi da suke bayyani kan dabi'ar kyakkyawar Niya, daga cikin misdakin wannan dabi'a shi ne niyar mumuni ta kasance cikin kokari wajen tabbatar da aiyukansa kamar yadda Allah madaukakin sarki yake so da kuma kaifiya ko yadda Annabin Rahama tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka suka koyar da mu, a cikin Littatafan Mahasin, Kafi da saurensu, an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) yayin da aka tambaye shi ma'anar Ibada sai yace:(kyakkyawar niya na da'a ko biyayya ta fuskar da ake yi masa biyayya) a wani hadisi na daban an bayyana cewa Imam (a.s) ya ce:( kyakkyawar niya na da'a ko biyayya ta fuskar da aka yi umarni da ita), Masu saurare, hakika Shekh Huru Amuly ya ware babe guda a cikin Littafinsa mai suna wasa'ilu Shi'a dangane da dabi'ar kyakkyawar Niya, sannan dukkanin hadisan da ya kawo a cikin wannan babe masu inganci ne, inda daga cikin jerin wadannan hadisi aka bayyana cewa kyakkyawar niya tana karfafa gangar jiki wajen aikata alheri, Imam Sadik (a.s) ya ce: (jiki baya raunana matukar an karfafa shi da kyakkyawar Niya), har ila yau masu saurare wannan dabi'a na daga cikin hanyoyin da suke yin sanadiyar shiga Aljanna, a cikin Littafin Amaly na shekh Tusy an ruwaito hadisi daga Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce:(Hakika Allah madaukakin sarki da karamcinsa da kuma falalarsa ya kan sanya Bawa Aljanna saboda gaskiya da kuma kyakkyawar Niyarsa), a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(duk wanda ya kudiri niyarsa, Allah madaukakin sarki zai lullube shi da niyar da ya kudiri aikatawa, idan ta kasance ta Alheri, sai a saka masa da alheri, idan kuma Sharri ne sai a saka masa da nufin sa na Sharri), kamar yadda daga cikin albarkar dake tattare da dabi'ar kyakkyawar niya da kuma neman alheri, rabauta da ladan aikin alheri da mumuni ya yi niya ko da kuwa wata larura ta gitta kuma ta zamanto tsani wajen aikata wannan alheri, a cikin Littafin Ilalu Shara'I'I an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce: (Hakika Bawa idan ya dauki Niyar yin sallar Nafilar Dare da Rana, sai ya kwanta, kwana ya ci karfinsa bai samu ya yi wannan salla ba, Allah madaukakin sarki zai rubuta masa ladan wannan salla, kuma ya rubuta masa ladan tasbihi a ko wani Linfashin da ya yi yayin barcinsa, sannan kuma ya sanya barcinsa a matsayin Sadaka) domin haka ne masu saurare, a wani hadisin aka bayyana cewa Niyar alheri da mumuni mai gaskiya zai yi, ta fi aikinsa domin Niyar tasa ta kan yi sanadiyar samun rabauta da Ladan da ba zai iya aikata aiki na alheri kamar sa ba, Har ila yau cikin Littafin Ilalu Shara'I'I an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce:(Niyar Mumuni ta fi aikinsa, domin shi Mumuni ya na niyar alheri mai girma wanda watakila ma ba zai iya aikata wa ba, Niyar Kafiri kuma ta fi shari da aikinsa domin shi kafiri yana niyar aikata sharri kuma yana zurfafa tunaninsa na aikata sharri da ba zai iya aikata shi har abada ba).
*************************Musuc******************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.