Mar 02, 2016 06:41 UTC
  • zababun aiyuka-Tauhidi

shiri ne dake bayyani kan mahimancin Tauhidi


Masu saurare Assalama Aleikum Barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirin zababbun aiyuka wanda ni Aminu Abdu zan gabatar da shi.


Sanannan abu ka ko wani Mutune , ko wani Dan Adam na  neman sani tare da bin  abubuwan da suka fi komai a ko wani fage  na rayuwa Hakika ko wani  Mutune a Duniya  na bayan abinda yafi a rayuwarsa, wannan itace tabi'ar Dan Adam


Hakika baya Nassosi na Shari'ar Musulinci sun amsa wannan tanbayar  managartat aiyuka sune suka fi komai a rayuwar dan adam kuma su ke sanya nutsuwa a cikin zuciya tare da samun Hakikanin jindadi na rayuwar Duniya da Lahira.


Bayan haka, Nassosi na musulinci sun koyar da mu fiyayun aiyuka kyawawa wanda a hakinkanin Gaskiya hakan na daga cikin tabbatuwar Rahama da Allah madaukakin sarki yayi a kan bayinsa domin a cikin a kwai Shiriya wadda zata kai Mutune zuwa fiyayyar rabauta na jin dadi da kuma yardar Allah madaukakin sarki a Duniya da Lahira.


Masu saurare wannan shiri zai dubu ne ga  wasu Hadisai tare  riwayoyi na musulci wadanda za su mana jagora wajen aikata fiyayun aiyuka wanda zasu sa mu samu rabauta a rayuwarmu ta Duniya da Lahira.amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan.


 


 


Musuc****************************************


 


Masu saurare shirin namu na yau zai fara ne da wasu hadisai dake ishara kan fiyayyun Ayyuka wanda za su man jagora zuwa ga hasken  Allah madaukakin sarki wanda a hakikanin Gaskiya wannan wata kauta ce da Allah subhanahu wa ta'ala ga bayinsa domin  samun shiriya da rabauta a Duniya da lahira .Hakika Sheik Saduk ya rawaito Hadisi daga Ma'aikin Allah kuma masoyinsa, Rahama ga Talikai baki daya Mustapha tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka cikin littafinsa mai suna Kitabul Sawabul A'amal wal Khisal inda a cikin wannan riwaya Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa abubuwa guda hudu duk wanda ya kasance a cikinsa zai kasance cikin Hasken Allah madaukakin sarki: na farko duk wanda ya kasance karshen Al'amuransa ya firta kalmar cewa babu wani abin bauta daga gaskiya sai Allah kuma ya shaida cewa ni Ma'aikin Allah ne ma'ana duk wanda ya kasance bisa kadonsa da mutuwa kuma karshen lokacin da zai koma ga Allah madaukakin sarki ya firta Kalmar cewa babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah kuma shaida cewa Annabi Muhamd Monzon Allah ne ,na biyu duk wanda wata Musiba ta samaishi zai ya ce daga Allah muke kuma  a gareishi za mu koma , na ukku duk wanda wani abun Alkhari ya same shi zai ce dukkan yabo ya tabbata ga Allah ubangijin Talikai na hudu duk wanda ya aikata kuskure zaice ina neman Gafara ga Allah sannan kuma ina tuba a gareishi.masu saurare wadannan sifoffi guda hudu sune Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka yace mana duk  ya kasance yana da su zai kasance cikin hasken Allah madaukakin sarki .


 


Musuc*********************************


 


Masu saurare barkanmu da sake saduwa , riwayarmu ta gaba za ta yi dubu ne kan fiyayun aiyuka wanda ke sanya Mutune ya kamala Hakikanin Imaninsa.Hakika Sheik Barki ya rawaito hadisi cikin Littafinsa mai suna Almahasin inda a cikin wannan Riwaya Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidan tsarkaka na cewa duk wanda ya cika Alwallarsa ya kyautata Sallarsa,ya kuma bayar da zakarsa ,ya kame fishinsa ko kuma ya hadiye fishinsa , ya kamai bakinsa daga fadar  magaganun marassa amfani ko kuma wadanda ba su  datse ba kuma ya nemi gafarar ubangijinsa dangane da kuskuran da ya aikata sannan ya yi aiki da Nasihar iyalan gidan Ma'aikin Allah , babu shakka ya kamala hakikanin Imani kuma Kofofin Aljanna a bude suke a gareishi.


 


Musuc********************************************


 


Masu saurare a nan shirin namu na yau zai dasa Aya sai kuma a Maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shiri idan Allah ya yarda muna rokon Allah madaukakin sarki da ya bamu dukkanin Alkhairinsa don Albarkacin iyalan Gidan Monzon Rahama Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka, a madadin Aminu Ibrahim Kiyawa da ya hada shirin aka saurara ni madugun shirin ni ke muku fatan Alkhairi wassalama aleikum wa rahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.