Mar 02, 2016 06:46 UTC
  • zababun aiyuka-falalar Tauhidi

shirin yana bayyani ne kan falalar tauhidi


Masu saurare Assalamu aleikum barka da warhaka barkanku da sake saduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi.shirin namu na yau zai dubu ne kan irin falalar da A…madaukakin sarki yayi ga bayinsa masu ambatonsa da aikata aiyuka na gari, inda shirin namu zai fara da falalar  Ambatar kalmar tauhidi mai tsarki  dangane da yadda take sanya farin ciki a zukata tare da kore duk facin rai ga duk wadanda suka dawamma ga anbatonta, amma kafin nan ga wannan.


 


Musuc******************************************


 


Hakika sheik Abu Ja'afaru Barki ya rawaito Hadisi a cikin littafinsa mai suna Almahasin daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare iyalan gidansa tsarkaka inda yake bayynawa  Sahabansa cewa  ku saurare shin kuna so in baku labarin abinda ya fi alkhairi a Duniya da Lahira wanda kuma idan  kuna cikin wata matsala ko bacin rai  kuka roki Allah maukakin sarki da wannan Kalmar, Allah zai yaye maku matsalarku cikin gaggawa. Sai sahaban Monzon Allah suka ce  Na'am ya ma'aikin Allah.sai Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka yace masu  kafin ku fara Addu'a kuce لا إله إلا الله ربنا لا نشرك به شيئاً wato babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah ubangijinmu ba ma hada bautarsa da kowa sannan sai ku roki abinda kuke so a wajensa ma'ana bayan kun anbanci Kalmar tauhidi sai ku meka bukatuntu wajen Allah madaukakin sarki da yardarsa za'a samu amsa cikin gaggawa.


 Har ila yau sikatul Islam kulaini ya rawaito hadisi cikin littafinsa mai suna  Alkafi wanda shima Sheik Saduk ya rawaito irin wannan hadisi a cikin littatafansa masu sunan Kitabul Tauhid da Kitabul Sawabul A'amal dukkaninsu daga shugabanmu Imam Muhamad Al'Bakir amincin Allah ya tabbata a gareishi yana cewa babu wani aiki  wanda yafi Girma a wajen Allah madaukakin sarki daga  cikin Aiyuku kuma ya fi yawan Lada kamar Kalmar Shahada wato cewa شهادة لا إله إلا الله ma'ana na shaida babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah sai Imam (a.s) ya ci gaba da cewa domin ba za a iya auna wannan kalama da komai ba sannan ba za'a iya daidaita Allah madaukakin sarki ba da komai ba  kuma babu  wani wanda zai iya tarayya da shi ga dukkanin Al'amuransa.


 


A cikin litattafain Almahasin,Kafi da kuma Sawabul A'amal an rawaito Hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare iyalan Gidansa tsarkaka na cewa duk wanda ya fadi kalamal لا إله إلا الله ma'ana babu wani abin bautawa da gaskiya  sai Allah za a dasa masa wata itaciya daga jan yakutu a cikin Aljanna kasanta daga farin Miski 'ya'yanta sunfi zuma zaki kuma sunfi kankara haske kuma sunfi turaren miski kamshi , Imam (a.s) ya ci gaba da cewa fiyayyar  Ibada itace  neman Gafara game da zunubai domin Allah madaukakin sarki yana cewa a cikin Alkur'aninsa mai Girma (surat Muhamad ayyat 19)Sannan ka sani Hakika cewa babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah,kuma ka nemi gabara game da zunubanka da kuma mumunai Maza da mumunai Mata , Allah kuma ya san makomarku da kuma matabbatarku.


Muna rokon Allah madaukakin sarki ya bamu ikon yin aiki da wannan hadisai mai tsarki don darajar Ma'aikin Allah tare da iyalan gidansa tsarkaka.


 


Musuc*****************************************


 


Masu saurare barkanku da sake saduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka , a ci gaban wannan shiri za su karanto wasu riwayoyi wadanda suke magana kan falala tare da Tasirin Salla wajen kusantar bawa ga Allah madauki sarki domin salla itace gimshikin Addini. Hakika Sheik Abu Ja'afaru Barki ya rawaito hadisi cikin littafinsa mai suna Almahasin daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka yana cewa Allah madaukakin sarki yace:babu abinda nafi so ga bawana kamar yin salla da na wajabtamasa tare da yadda bawana zaiyi  ta yin  sallolin  Nafila domin samun soyyayata idan har ya samu  wannan samu wannan soyayyar to zan kasance masa jinsa wanda yake ji da shi ,idanunsa wanda yake kallo da shi , harshensa wanda yake magana da shi, hanunsa wanda yake aiki da shi kafar sa wanda yake tafiya da ita kuma duk lokacin da ya kirani zan amsa masa kuma idan ya tambayeni zan bashi.


 


Masu saurare fiyayar salla wanda Allah madaukakin sarki ya fi so ga bayinsa wanda a kayi don soyayya da godiya a gareishi ko ya kasance sallar ta Farilla ce ko kuma Nafila kamar yadda riwayar da  babban Malamin nan أبوالحسن الحراني    ya rawaito cikin littafinsa mai suna Tukhuful Ukul an Aly Rasul (s.a.w.s) daga shugabanmu Imam Husain (a.s) yana cewa: Hakika wasu Mutane suna bautawa Allah saboda kodayin Lada ko kuma Aljanna, irin wannan Ibada  ita ce Ibada kasuwanci, wasu kuma suna bautar Allah saboda tsoransa irin wannan ibada itace ibadar Bayi ga mahilicinsu, wasu suna bautawa Allah  don soyayyarsa tare gode masa wannan ibada itace ibadar 'yantartu kuma itace fiyayyar Ibada wadda  da tafi tasiri wajen daukaka bawa zuwa martabar kamala tare da kusantar da shi ga ubangijinsa.


 


Masu saurare anan za mu dasa aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe  sai  kuma a maku na gaba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shirin, a madadin Aminu Ibrahim kiyawa da ya hada shirin aka saurara muke muku fatan Alkhairi wassalama aleikum warahamatullahi wa barkatuhu.