Dec 18, 2016 05:44 UTC

Shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,

Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, a Shirin da ya gabata mun yi bayyani kan mahimancin dabi'ar kyakkyawar Niya, Shirin na Yau ma zai yi bayyani kan dabi'ar yawaita kyakkyauta a Rayunwa da kuma nisanta daga mumunar niya da neman sharri, domin yin hakan na daga cikin kyawawen dabi'un musulinci,amma kafin shiga shirin ga wawann.

*************************Musuc*****************************

Masu saurare,Shirin na Yau zai fara da Hadisin Manzon Rahama Mahamadu Dan Abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka inda ya ce:(babu fata sai ga Alheri mai yawa) wannan riwaya ta zo ne cikin Littafin Ja'afariyat, har ila yau a cikin wannan littafi, an ruwaito hadisi daga Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce:(Idan dayanku zai yi fatan to ya kasance fatansa na alheri ne, kuma ya yawaita shi, domin shi Allah mai buwaye ne mai karamci) a cikin Littafin Fikdu Ridha, an ruwaito wani hadisi daga Imam (a.s) na cewa (Niyar Mumuni ta fi alheri ga aikinsa domin shi ya niyar abu mafi alheri da aikinsa,kuma domin shi ya niyar alherin da ya fi karfinsa kuma ba zai iya aikata shi ba), Masu saurare, Hadisai da dama sun shiryar da mu cewa daga cikin rahamar Ubangiji yana taimakawa masu irin wannan kyakkyawar dabi'a wajen idrakin abinda ba za su iya aikatawa na alherin da suka yi niyar aikata shi cikin gaskiya da ikhlasi, Hakika Shekh Mufid cikin Littafinsa Amaly ya ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:( Hakika Allah madaukakin sarki ya kaddara Taimakonsa daidai gwalgwado da niyarsu, idan Bawa ya kyautata Niyar sa taimakon Allah ya cika a gare shi, wanda kuma niyarsa ragaggata ce, taimakon zai kasance ragagge daidai gwalgwadon Niyarsa), a cikin Littafin Amaly na Shekh Tusy an ruwaito hadisi daga Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce:(Duk wanda ya yi niyar aikata wani abu da Allah tabarka wa ta'ala ya yarda da shi, Allah zai bayyana masa shi kuma ya yassare masa aikata shi) har ila yau cikin Littafin Fikdu Ridha (a.s) an ruwaito Hadisi daga Imam (a.s) na cewa:(Babu wani Bawa da zai kudiri niyar aikata alheri, har ranaikun da ya kudiri aikata wannan alheri su zo su fice face Allah madaukakin sarki ya bayyana masa alheri, kuma babu wani Bawa zai kudiri niyar aikata Shari, har ranaikun da ya kudiri aikata wannan sharri su zo su fice face Allah madaukakin sarki ya bayyana masa sharrinsa). Masu Saurare, a bangare guda wasu hadisai na daban sun tsoratar da mu kan mumanan sakamako na mumunar niya da neman Sharri, watau fatan abinda babu yardar Allah tabaraka wa ta'ala a cikinsa, Hakika cikin Littafin Amaly na shekh Tusy, an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(duk wanda ya kudiri niyar aikata aikin da a kwai fishin Allah cikin sa, Allah tabaraka wa ta 'ala zai bayyana masa abinda zai sanya masa bakin ciki), kuma hakika mumunar dabi'a ta neman shari ga mumuni ya kai yin sanadiyar rashin samun karbuwar aiki na Mutum ko da kuwa aikin alheri ne, a cikin Littafin Fikhu Ridha(a.s) an ruwaito hadisi daga Imam (a.s) na cewa:(Allah tabaraka wa ta'ala ba ya karbar aikin Bawa da a cikin zuciyarsa a kwai wani mumunan nufi ga Mumuni) har ila yau niyar Sharri na daga cikin ababen da suke rage arzikin Bawa, a yayin da kuma kyakkyawar Niya take kare arzikin Bawa, a cikin Littafin Mahasin, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(Duk wanda ya kyautata niyarsa Allah madaukakin zai kara masa arzukinsa), a cikin Littafin Ikabul-A'amal,an ruwaito hadisi daga Imam (a.s):(Hakika Idan Mumuni ya kudiri niyar aikata zunubi sai a hana masa Arzukinsa).

*******************Musucc**************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran,ci gaban shirin zai yi bayyani kan Ikhlasi a cikin Niya, watau Mumuni ya yi kokari wajen sanya kusanci da kuma neman yardar Allah a aikinsa, alamar wannan kyakkyawar dabi'a kumwa itace kadda Bawa ya yi kokari wajen neman Yabo a aikin da ya yi saboda Allah.Hakika babban malamin nan masanin Allah Ibn Fahad Alhilly, da kuma Shekh Abul futuh Arrazy cikin tafsirinsa, an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce:(Hakika ka ko wata gaskiya a kwai gaskiya, kuma babu wani bawa da zai cimma wata gaskiya kamar Ikhlasi ta yadda ba zai so ba a gode masa bisa komai a kan wani aiki da aikata), har ila yau daga cikn girman albarkar dake tattare da dabi'ar ikhlasi ,shi ne samun rabauta da soyayyar Allah madaukakin sarki.wannan shi ne abinda Hadisin Kudisi da aka ruwaito cikin tafsirin Shekh ibn Futuh Arrazy wanda aka fi sani da tafsiru Ruhu Janan ya yi mana albishir da shi,an ruwaito hadisin  ne daga Huzaifatu bn Yaman ya ce:(Na tambayi Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka dangane da Ikhlasi, sai ya ce Na tambayi irin wannan tambaya daga Jibrilu, sai ya ce:Allah madaukakin sarki ya ce Ikhlasi Sirri ne daga cikin sirrina na nake sanya wa a zuciyar wanda nake So). Kamar yadda yake Ikhlasi mabudin karbar Aiyuka ne , an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce:(Bawa ba zai kasance mai bautar Allah hakikanin Ibada ba har sai ya yanke dukkanin fatansa na neman yabo daga wajen halittu, a wannan lokaci sai madaukakin sarki ya ce: wannan aiki an yi shi ne domin ni sai Allah ya karbe sa cikin karamarsa), Ya zo kuma cikin wani hadisin Kudisi wanda aka ruwaito cikin Littafin Fikhu Ridha (a.s) inda a cikin sa aka ce Allah tabaraka wa ta'ala na cewa    (Ni ne mafi alheri sharike, duk kuwa wanda ya yi shirka da ni ga wani Na cikin wani aiki b azan karba sai dai wanda ya kasance an yi shi Dan Ni kadai). Har ila yau daga cikin girman albarkar da mai wannan kyakkyawar dabi'a zai samu, Hakika Hadisai da dama sun bayyana shi a matsayin mafi girman Ni'imar Allah madaukakin sarki ga Mutum, kamar yadda ya zo cikin hadisin da aka ruwaito daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce: (Allah madaukakin sarki ba zai yi gaggauta yiwa Bawan da ya kasance cikin Zuciyar sa a kwai wanin Allah, kuma mafin girma da karamar aiyuka shi ne kusanci ga Bautar Allah madaukakin sarki). A cikin Littafin Kafi an ruwaito Hadisi, inda a cikin sa aka tambayi Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) dangane da fadar Allah madaukakin sarki (Sai dai Wanda ya zo wa Allah da tsarkakakkiyar Zuciya) Suratu Shu'ara'I Aya ta 89. Sai Imam (a.s) ya amsa da cewa tsarkakakkiyar Zuciya ita ce wacce ta hadu da Ubangijinta babu ko a cikin cikinta face shi, dukkanin Zuciyar da akwai shakku ko yiwa Ubangiji Kishiya a cikinta ta fadi, kuma Hakika Bayin Allah na gari sun zabi Zuhudu ko gudun Duniya a cikin wannan Duniya kararriya domin su danganta zukatantu da Lahira).Masu saurare har ila yau daga cikin albarkar dake tattare da dabi'ar Ihklasi ga Allah madaukakin sarki a dukkanin aikin da Mutum zai yi, shi ne gaggauta samun sakamakon sa, kuma Hakika duk abinda ya kasance saboda Allah tofo yake, Hakika cikin litattafan Almahasin da Kafi an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Muhamad Bakir (a.s) ya ce:(babu abinda ya banbanta tsakanin gaskiya da karya face karamcin Hankali, sai aka tambaye shi yaya hakan zai kasance Ya Dan Ma'aikin Allah? Sai amincin Allah ya tabbata a gare shi ya ce: Hakika Bawa zai aikata wani aiki wanda akwai yardar Allah a cikin sa kuma yana nufi da shi wanin Allah, da ya aikata wannan aiki saboda Allah da ya samu abinda yake bukata cikin gaggauwa daga wannan).

*********************Musuc***************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.