zababun Aiyuka-Soyayya ko kiyayya saboda Allah
shirin zai yi dubu kan Soyayya ko kiyayya saboda Allah madaukakin sarki
Masu saurare Assalamu aleikum barka da warhaka barkanku da sake saduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi. shirin namu na yau zai dubu ne kan Soyayya ko kiyayya saboda Allah madaukakin sarki amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan
Masu saurare an rawaito hadisai da dama cikin littatafai masu inganci daban daban kan mahimancin Soyayya saboda Allah ko kiyayya saboda shi a cikin wata riwayar Monzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan Gidansa tsarkaka na cewa fiyayyar kusancin shedu na ban gaskiya Soyayya saboda Allah ko yin kiyayya saboda Allah.
Har ila yau a cikin Littafin Adda'awat na Sheik Kutbuddin Arrawandi an rawaito hadisi makamancin wannan, inda a cikin wannan riwaya aka ce Allah madaukakin sarki yace ma Annabi Musa (a.s) ya kai Musa wani Aiki ne ka yi domin ni ? Sai Annabi Musa (a.s) yace Ya Ubangijina nayi salla nayi azumi na bayar da sadaka ko kuma na bayar da zakka sannan nayi ta ambatonka diyawa sai Allah madaukakin sarki yace masa salla da kayi hujja ce a gareika,azimi kwa Garkuwa ne a gareika, sadaka da zakka su kuma Haske ne,kuma ambatona da kace kayi ay fadodinka ne ka gina a gidan Aljanna (ganin cewa dukkanin wadannan aiyuka amfaninsu na komawa da wannan yayisu )sai Allah madaukakin sarki ya ci gaba da cewa Annabi Musa (a.s) wani aiki ne kayi sabo da ni?sai Annabi Musa (a.s) yace Ya Ubangijina nuna mini aikin da zanyi ya zamnto sabo da kai wato zai kasance na kane kawai sai Allah madaukakin sarki yace masa Ya Musa shin ka yi soyayya sabo da ni wato kaso wani saboda ni ko kuma ka ki wani sabodani (kamar yadda mai Ahdari ke cewa kaso Mutune Don Allah wato saboda yaso Al'amarin Allah kuma kaki Mutune Dan Allah wato Don yaki Al'amarin Allah) daga nan sai Annabi Musa (a.s) ya gane da cewa fiyayyen aiyuka shine Soyayya saboda Allah da kuma kiyayya saboda Allah.
Har ila yau sheik Saduk (RTA) ya rawaito hadisi cikin litattafansa wato Alkafi da kuma Al'amaly dangane da wannan aiki mai Albarka wanda ya zamanto wasila ne na zama zababbun bayi a wajen mahalicinsu.Masoyin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa Soyayyar Mumuni ga dan uwansa mumuni don Allah , daya ne daga cikin mafi girman imani ko kuma girma na bada Gaskiya kuma duk wanda ya so saboda Allah kuma ya ki saboda Allah sannan ya bada dan Allah kuma ya hana don Allah yana daga cikin zababbu bayi a wajen Allah madaukakin sarki.
Muna rokon Allah madaukakin sarki da ya bamu ikon yin aiki saboda shi.
Musuc**************************************
Masu saurare barkanku da sake saduwa , a ci gaban shirin zamu kawo muku wasu hadisai da suka shafi salla saboda Salla na daga cikin fiyayyun aiyuka masu kusantar da Bawa ga Allah madaukakin sarki bayan wulaya kamar yadda sheik Abu Ja'afarur Barki ya rawaito cikin littafinsa mai suna Almahasin daga salihin bawan nan wato Zurara bn A'ayun wanda ya rawaito daga Imam Bakir (a.s)yana cewa an gina musulinci a kan abubuwa guda biyar: salla , Azumu, Zakka, Haj da kuma Wulaya zai Zurara ya tambayi Imam Bakir (a.s) wane ne daga ya fi?sai Imam(a.s) yace masa Wulaya c eta fi domin itace ma budinsu domin waly shine hujarsu ko kuma dalili a gareisu sai Zurara yace sai na cigaba da Tambayar Imam wannene ke bin wulaya wajen fifiko ?sai Imam (a.s) yace Salla domin Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare iyalan gidansa tsarkaka yace Salla itace Gimshikin Addininku.
Har ila yau an rawaito irin wannan Hadisi a cikin Littafin Kafi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s)inda yake cewa Salla Gimshikin Addini ce kamar yadda idan Gimshikin Runfa suka ginu da kwai abinda aka rufawa runfar kamar zana da igiya za su zauna da kwau haka zalika idan salla tayi kwau duk wasu aiyuka da za su biyu baya za su yi kwau. Kamar yadda wasu hadisai da dama suka bayyana cewa fiyayyen aiyuka bayan sanin Allah da waliyansa yin salla a farkon lokaci .sheik Kutubuddin Alhusaini Arrawandi ya rawaito hadisi cikin Littafina mai suna Kitabudda'awat inda yace Mu'awiya bn Wahab ya tambayi Aba Abdullahi Sadik (a.s) kan cewa wani aikini yafi kusantar da bayi ga mahalicinsu sai Imam (a.s) ba san wani aiki ba wanda yafi yin salla a farkon lokaci bayan sani (wato sanin Allah da annabawa tare da waliyansa saboda sai kasan Allah zaka bauta mashi kuma ta hanyar annbawa ce tare da waliyan Allah ake sanin Allah har ma a bauta mashi.sai Imam Sadik (a.s) ya ci gaba da cewa shin ba ka gab a abinda Annabi Isa Dan Maryamu (a.s) yace Ubangijina ya umarce ni da yin Salla da bada Zakka matukar inada rai.kuma an tambayi Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi game da fiyayun aikuka sai yace salla a farkon Lokacinta.
Har ila yau Imam Sadik(a.s) yace duk wanda yayi Sallar Farida shi bako ne a wajen Allah kuma Hakki ne ga Allah madaukakin sarki na ya girmama bakonsa.
Nutsuwa a Salla na daga cikin abubuwan da aka yi Umarni a cikin salla kamar yadda Imam Sadik (a.s) ya bayyana a cikin Littafin Attahzib yayin da Abu Hanifa ya tambayeshi inda yace na tambayi Imam Sadik (a.s) kan cewa yin kuka a salla na iya batata? Sai Imam Sadik (a.s) yace masa idan ya kasance kukan na tuna Lahira ne to shine abinda ake so amma idan ya kasance don tuna wani dan uwanka ne da ya mutu to wannan yana bata salla.
Masu saurare anan za mu dasa aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shirin, a madadin Aminu Ibrahim kiyawa da ya hada shirin aka saurara muke muku fatan Alkhairi wassalama aleikum warahamatullahi wa barkatuhu.