Mar 04, 2016 02:11 UTC
  • zababun Aiyuka-falalar yin Salati ga Manzon Allah

shirin zai yi dubu kan falalar yin Salati ga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka


Masu saurare Assalamu aleikum barka da warhaka barkanku da sake saduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka wanda ni Aminu Abdu ke gabatar da shi. A shirin day a gabata munyi magana ne kan mahimancin Salla da kuma yenta a farkon lokaci, a shirin namu nay au kuma  za muyi magana ne kan falalar yin Salati ga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka, amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan


 


Musuc**********************


 


Masu saurare da farkon za mu fara ne da wasiyar ma'aikin Allah (S,a ,w,a) na cewa babbar wasila zuwa ga rahamar ubangiji itace yin salati a gareishi inda yake cewa (ku yawaita yin salati a gareini domin yin Salati a gareini  haskeni a cikin Kabari,kuma haske ne a kan Siradi, kuma haske ne a cikin Aljanna).


A kusa da wannan riwaya السيد الجليل قطب الدين الراوندي – رضوان الله عليه  a cikin littafinsa mai suna الدعوات ya nakalto wata riwaya daga cikin irin bisharorin da Manzon Rahama tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka yayi mana inda yake cewa (duk wanda yayi min salati so uku a ko wata rana da ko wani dare don soyayya a gareni to Allah madaukakin sarki zai gafarta masa dukkanin zunubansa na wannan rana da na wannan Dare.


Har ila yau an rawaito wani hadisi daga  shugabanmu Imam Sadik (a.s) yana cewa:(duk wanda yayiwa Annabi Salati tare da iyalan gidansa tsarkaka so guda tare da niya da kuma Ihklasi Allah madaukakin sarki zai biya masa bukatunshi guda Dari, talatin a nan Duniya kuma sauren saba'in din a ranan Lahira.


 


Masu saurare idan muka yi nazari a kan wannan riwayoyi da ma wasu hadisan da aka rawaito daga cikin manyan litattafai masu inganci daga ciki kwa hard a littafin nan mai suna شرح الأخبار للقاضي النعمان المغربي tare da sanadinsa daga Abi Alkama inda yace wata rana Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya yi masa Sallar Assubahi, bayan an gama sallar sai Ma'aikin Allah ya juyo sannan yace mana shin kuna so in baku labarin abinda na gani a cikin barcina na jiya? Sai Iy ya Ma'aikin Allah…sai Monzon Allah yace naga kawuna Hamza da kuma Dan Kawu na Ja'afar yardar Allah ta tabbata a gareisu hakika kun rigamu zuwa Lahira kuma kunyi aiki a nan Duniya ko wani aiki ne yafi a nan Duniya?ku bani labarin wani aiki ne  kuka tarda a lahira wanda yafi fifiko? Sai suka ce mun sadaukar da  Ubanninmu  tare da uwayenmyu saboda kai  zabbbun aikunan da muka samu sune na farko yin salati a gareiku,shayarwa da ruwa ga mabukata, Soyayyar Aliyu bn Abi Talib (a.s). a cikin wata riwaya kwa bayan an ce Soyayyar Aliyu bn Talib (a.s) sai aka ce bayar da Sadaka a boye.muna rogon Allah madaukakin sarki da ya bamu damar aikata wadannan aiyuka.


 


Musuc********************


 


Masu saurare barkanku da sake saduwa, bayan munyi magana kan falalar yin Salati ga Maonzin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka za mu ci gaba da shirin tare riwayoyi masu ishara dangane da  falala na  kautatawa Dan uwa musulmi wanda shima na daga cikin zababbun aiyuka wanda za su mana jagora wajen samun rabauta a Duniya da lahira.kamar yadda hadisai da dama suka  yi ishara da hakan inda aka ce daga cikin aiyuka masu yawan Lada da Albarka,kautatawa ga Dan uwa musulmi kamar yadda sheik Amady ya rawaito hadisi daga shugabanmu Amirir mumunin Aliyu bn Abi Talib (a.s) a cikin Littafinsa mai sunaغرر الحكم inda riwayar ke cewa fiyayyar kautata itace ka taya Dan uwanka musulmi yin bakinciki yayin da yake cikin bakin ciki haka zalika ka ta yashi barin cikin yayin da yake cikin farin ciki ,yin haka shine shine fiyayen kautatawa a wajen Allah madaukakin sarki).


 A bangare guda kuma Sheik Saduk (r.t.a) ya rawaito hahisi a cikin Littatafansa masu sunan الأمالي وعيون أخبار الرضا – عليه السلام  daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da iyalan gidansa tsarkaka inda yace: daya daga cikin zababbun aiyuka a wajen Allah madaukakin sarki sanyaya zukatan da suka yi zafi wato mutuwan da ransa ya bace sanadiyar wani abu a matsayin na dan uwansa kaje ka lallasheshi har ya sauka ma'ana ya dawo hayyacinsa. Sannan kuma hadisin ya ci gaba da cewa, da kuma kosar da cikkuna masu yunwa,wato ciyar da Mutanan da suke bukatar abinci ko kuma suke jin yunwa sai hadisin ya ci gaba da cewa na rantse da wanda ran Muhammadou ke hanunsa babu wani bawa da yayi imani da ni zai kona cikinsa a cike sannan kuma ya bar Dan uwansa musulmi cikin yunwa, a wani hadisin kwa an ce ya bar makobcinsa cikin yunwa.


Har ila yau masu saurare mu dibi irin Albarkar da Allah madaukakin sarki ya sanya a irin wannan aiki cikin riwayar da mu karanto wadda sheik Sarwi ya rawaito cikin littafinsa mai suna Almunakib daga Imam husaini bn Ali (a.s) inda yake cewa babu shakka ya tabbatu a gareini maganar da ma'aikin Allah yayi na cewa fiyayen aiki a wajen Allah bayan salla sanya farin ciki a cikin zukatan mumunai idan bai sabawa hukuncin ubangiji ba, wata rana na hadu da wani bawa yana cin abinci da wani Kare  (ma'ana idan yaci loma guda sai ya dauki makamanciyarta ya baiwa wannan kare) sai na tambayashi ko mi yasa ya ke baiwa wannan kare abinci, sai yace mani ya Dan Ma'aikin Allah ina cigin facin rai ne don haka ina neman farin ciki ne da walwalar wannan kare don haka nike raba abinci na tare da wannan kare saboda mai gidana bayahude ne ni kuma ina so in rabu da shi. Sai Imam Husain (a.s) ya ci gaba da cewa sai nafi wajen Bayahudan wato mamalakin wannan bawa tare da Dinare dari biyu a matsayin kudin baya sai wannan bayahudan yace mani na barmaka wannan bawa kuma wannan Garkar tashi ce don na medo maka kudunka.sai Imam (a.s) yace ni kuma na bar maka wannan kudi, sai Bayahudan yace na amince ni kuma na baiwa wannan bawa kudin. Sai Imam Hussain (a.s) yace na yantar da wannan bawa tare da dukkanin wannan dukiya sai Matar Bayahudan tace na musulinta kuma na yafewa mijina Sadakina (domin sadaki na wasu kabilun ya babbanta ana dora sadaki ne mai yauni sai lokacin da za a rabu a ke biyan sadakin )


Shima Bayahudan yace nima na musulinta kuma na baiwa matata wannan Gida ma'ana gidan da suke ciki.


 


Musuc************************************


 


Masu saurare anan za mu dasa aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe  sai  kuma a maku na gaba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shirin, a madadin Aminu Ibrahim kiyawa da ya hada shirin aka saurara muku fatan Alkhairi wassalama aleikum warahamatullahi wa barkatuhu.